Kwankwaso da Obi Sun Samu Babbar Dama a Kwamitin Yakin Neman Zaben NDC
- NDC ta ce tana kan gaba wajen shawarwari domin kafa da ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Kasa, Peter Obi, da abokin takararsa Rabiu Musa Kwankwaso
- Jam’iyyar ta bai wa Obi da Kwankwaso damar zaɓar wasu daga cikin manyan jami’an kwamitin, ciki har da Darakta-Janar da kakakin yaƙin neman zaɓe
- NDC ta bukaci ’yan takararta da ƙungiyoyin magoya bayansu su guji rikicin cikin gida, su mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta ce tana gudanar da shawarwari domin kafa wa da ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Kasa, Peter Obi.
Jam’iyyar ta kuma ce Obi da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, an ba su damar gabatar da sunayen mafi yawan manyan jami’an kwamitin.

Source: Facebook
Obi da Kwankwaso sun gana da shugabannin NDC
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Osa Director Esq, ya sanya wa hannu.
NDC ta ce Obi da Kwankwaso sun gudanar da taruka da jagoranta na kasa, Sanata Henry Seriake Dickson, da sauran shugabannin jam’iyyar.
NDC ta ce an riga an shirya cikakken tsarin gudanar da kwamitin yaƙin neman zaɓen tun watan Agusta, sannan aka miƙa shi ga Obi da Kwankwaso domin su duba tare da ba da shawarwarinsu.
Ta ƙara da cewa an kuma karɓi shawarwari da sunayen da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na ƙasar suka gabatar.
“Shugabancin jam’iyyar ya bai wa ɗan takarar shugaban ƙasa da abokin takararsa damar gabatar da sunayen jami’an da suke so,” in ji sanarwar.
Mukaman da Obi da Kwankwaso za su zaɓa
A cewar NDC, Obi da Kwankwaso za su gabatar da sunayen Darakta-Janar, Mataimakin Darakta-Janar na Arewa, Kakakin yaƙin neman zaɓe da mataimakinsa.

Kara karanta wannan
Sojoji sun cafke kwamandojin 'yan ta'adda da ke da hannu a kisan babban janar a Katsina
Haka kuma, za su zaɓi shugaban sashen sababbin kafofin yaɗa labarai, daraktan kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe da mataimakinsa, da sauran manyan jami’ai.
Jam’iyyar ta ce Daraktan Kuɗi da mataimakinsa za su yi aiki tare da Ma’aji na Ƙasa domin kula da kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe, jaridar The Punch ta kawo labarin.
NDC ta yi bayanin yadda za a kula da kuɗaɗen kamfen
Jam’iyyar ta ce tsarin an ƙirƙire shi ne domin tabbatar da gaskiya da bin ƙa’idojin bayar da rahoton kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe da dokar zaɓe ta tanada.
Ta ce duk kuɗaɗen da za a tara domin yaƙin neman zaɓen za a saka su cikin wani asusun banki na musamman na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa.
NDC ta ce jami’an da ɗan takarar shugaban ƙasa, abokin takararsa da ma’aji na kasa na jam’iyyar suka zaɓa ne za su kula da asusun.
An ɗage ƙaddamar da kwamitin
Jam’iyyar ta ce ta riga ta tsara jadawalin gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓe, amma ana jiran kammala shirye-shiryen tara kuɗaɗen kamfen da tsarin samar da su, waɗanda ’yan takarar za su jagoranta.
An shirya ƙaddamar da kwamitin a makon farko na watan Satumba, amma aka ɗage shi saboda jadawalin tafiyar Obi.
NDC ta ce za ta sanar da ranar ƙaddamar da kwamitin tare da rantsar da jami’ansa da zarar Obi da Kwankwaso sun miƙa sauran shawarwarinsu.

Source: Facebook
Gwamnatin Abba ta bude kofar sulhu da Kwankwaso
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf a shirye take ta yi sulhu da jagoran Kungiyar Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso.
Gwamnatin Abba ta bayyana cewa tana kallon tsohon gwamnan a matsayin uba, don haka za ta marabci duk wani yunkuri na dawo da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu.
Asali: Legit.ng

