Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Man Fetur Ya Sake Gamuwa da Cikas gabanin Zaben 2027

Shirin Atiku na Dawo da Tallafin Man Fetur Ya Sake Gamuwa da Cikas gabanin Zaben 2027

  • Masanin harkokin tattalin arziki, Mustafa Chike-Obi ya ce shirin Atiku na dawo da tallafin man fetur ba zai yi aiki yadda ya kamata ba
  • Tsohon shugaban bankin Fidelity ya ce hakan na iya jawo asarar dimbin arzikin Najeriya ta fuskar musayar kudaden waje
  • Ya ba da shawarar amfani da takardun tallafi ga ‘yan Najeriya masu karamin karfi maimakon tallafin da ya shafi kowa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon shugaban Fidelity Bank, Mustafa Chike-Obi, ya ce shirin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur babbar matsala ce ga Najeriya.

Masanin harkokin tattalin arzikin ya ce dawo da tallafin fetur na iya jawo kashe rabin arzikin Najeriya wajen musayar kudaden waje.

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar a wurin kaddamar hadakar yan adawa a ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Chike-Obi ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a shirin Policy Without Politics da aka wallafa a Facebook, wanda yake gabatarwa tare da Ken Ikpe, babban jami’in gudanarwa na Graviti Hill Limited.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Atiku ya bayyana dalilin da ya sa yake son dawo da tallafin fetur

A ranar 19 ga Agusta, Atiku, dan takarar shugaban kasa na ADC ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a shekarar 2027.

Chike-Obi ya soki shirin Atiku

Da yake mayar da martani kan shirin, Chike-Obi, wanda shi ne babban shugaba na farko a kamfanin AMCON, ya bayyana maganar Atiku a matsayin “rashin fahimta.”

Ya ce idan Najeriya za ta iya sayar da danyen mai kan dala 100 a kowace ganga, amma ta zabi sayar da shi ga wani a kan dala 50, hakan na nufin kasar ta kashe rabin arzikin da take samu.

“Idan ana sayar da danyen mai kan dala 100 a kasuwar duniya, sannan ka ce kai za ka sayar da shi ga wani kan dala 50 bisa tsarin tallafi, to ka kashe rabin arzikin kasa," in ji shi.

Illolin dawo da tallafin mai a Najeriya

Tsohon shugaban AMCON ya ce dawo da tallafin man fetur zai bude damar da masu samar da mai za su rika samun ribar kai kaya zuwa kasashen waje ta hanyar safara.

Kara karanta wannan

Atiku zai rattaba hannu kan dawo da tallafin man fetur da yan Najeriya

Chike-Obi ya ce gwamnati za ta kuma bukaci kafa tsarin kula da farashin man fetur tare da sanya ido sosai kan masu samar da shi domin hana fitar da man da aka ba da tallafi zuwa kasashen waje ko safarar sa ba bisa ka’ida ba.

Ya kara da cewa gwamnati za ta kuma bukaci kafa tsarin kayyade farashi da na sa ido kan harkokin masu samar da man, kamar yadda The Cable ta kawo.

Ya ce irin wannan tsarin zai sanya gwamnati ta kashe dimbin albarkatu wajen kula da wani abu da ya kamata a bar yan kasuwa suntafiyar da shi.

Fetur.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da yadda ake zuba fetur a gidan mai Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Masani ya kawo mafita ga Najeriya

A maimakon dawo da tallafin, Chike-Obi ya ba da shawarar cewa gwamnati ta yi amfani da takardun shaidar tallafi ga ‘yan Najeriya masu karamin karfi idan har ta yanke shawarar dawo da wani nau’in tallafi.

Ya ce gwamnati za ta iya tantance kudin shiga na mutane domin gano wadanda suka cancanci samun tallafin, sannan ta ba wadanda ke kasa da wani matakin kudin shiga takardun tallafi.

Atiku zai bude iyakokin Najeriya

Kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai sake bude iyakokin Najeriya da kasashen makwabta idan aka zabe shi.

Atiku ya ce rufe iyakokin kasa ya jefa matasa da dama cikin rashin aikin yi tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci tsakanin kasashe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262