An Bukaci Tinubu Ya Hakura da Shiga Takara a Zaben 2027

An Bukaci Tinubu Ya Hakura da Shiga Takara a Zaben 2027

  • Jam’iyyar APM ta buƙaci Bola Tinubu ya janye daga takarar shugaban ƙasa ta 2027 har sai an warware tambayoyin da suka shafi zargin alaƙarsa da miyagun ƙwayoyi a Amurka
  • Jam’iyyar ta yi nuni da shigar da kara da aka yi a kotun Amurka da ke Washington, D.C., kan neman a saki wasu bayanai da ake zargin suna da alaƙa da shugaba Tinubu
  • A bayanan da APM ta yi, ta ce Najeriya na buƙatar shugaban ƙasa wanda tarihinsa ba shi da wasu tambayoyi da ba a warware ba kan gaskiya da amana a tarihinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar APM ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sake tunanin neman wa’adi na biyu a 2027, tana mai cewa akwai wasu tambayoyi da ba a warware ba kan zargin alaƙarsa da wani binciken miyagun ƙwayoyi a Amurka.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan bukatar Atiku ta hana Tinubu takara a 2027

Jam’iyyar ta ce ya kamata Shugaban ya bayyana gaskiya kan batun kafin ya nemi sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Lokacin da APC ta ba Bola Tinubu shaidar lashe zaben fitar da gwani. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Maganar APM kan Tinubu

Daily Trust ta wallafa cewa sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Abubakar, ya ce APM ta jingina matsayinta da wani zaman da aka yi a ranar 28 ga Agusta 2026 a kotun Amurka.

Ana neman a saki wasu takardu daga Hukumar Binciken Amurka (FBI) da Hukumar Yaki da Miyagun Ƙwayoyi (DEA), waɗanda ake zargin suna da alaƙa da Shugaba Tinubu.

APM ta ce ƙoƙarin lauyoyin Tinubu na adawa da yanke hukunci cikin gaggawa da kuma hana sakin takardun ya ƙara haifar da tambayoyi game da batun.

Jam’iyyar ta zargi lauyoyin Shugaban da ƙoƙarin dakatar da shari’ar da kuma hana fitar da bayanan da take ganin suna da muhimmanci ga jama’a.

The Sun ta wallafa cewa APM ta ce idan har Shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa babu wani abu mai zargi a cikin takardun, bai kamata a samu wata matsala wajen goyon bayan sakin su ba.

Kara karanta wannan

Mata ta kalli tawagar APC ido da ido, ta ce ko kuri'a 1 ba za su samu ba

Maganar takarar Tinubu a 2027

A ƙarshe, jam’iyyar ta roƙi Shugaba Tinubu da ya sake duba shirin neman wa’adi na biyu har sai an warware wannan ce-ce-ku-ce.

APM ta ce Najeriya na buƙatar Shugaban da ba ya fuskantar tambayoyi da ba a warware ba kan zamba, cin hanci da rashawa ko rashin gaskiya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya tare da mataimakinsa, Kashim Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ta kuma yi kira ga sauran masu neman takarar shugaban ƙasa da su kasance cikin shiri domin jama’a su binciki tarihin su yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.

Batun shari'ar Atiku da Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya shigar da ƙara a Kotun Tarayya da ke Abuja yana neman a hana Shugaba Bola Tinubu tsayawa takarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Atiku ya kalubalanci cancantar Tinubu ne bisa zargin cewa takardar shaidar kammala aikin yi wa ƙasa hidima ta NYSC da aka miƙa wa INEC na ɗauke da wani suna daban da sunan shugaban.

A yayin da aka ambaci shari’ar, lauyan mai ƙara, Joseph Onu, ya shaida wa kotun cewa ya kasa miƙa takardun ƙarar kai tsaye ga wanda ake ƙara, don haka yake son a ba shi damar yin hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng