Ana Shirin Zaben 2027, Gwamna Ya Nada Sababbin Hadimai Sama da 100

Ana Shirin Zaben 2027, Gwamna Ya Nada Sababbin Hadimai Sama da 100

  • Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah ya amince da naɗin sababbin hadimai 101 da suka haɗa da masu ba shi shawara da manyan mataimaka
  • Sababbin naɗin sun ƙunshi masu ba da shawara na musamman bakwai, manyan mataimaka shida da mataimaka na musamman 88
  • Sakataren Gwamnatin Jihar Enugu ya bayyana cewa wadanda aka nada za su ya fara aiki nan take

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Enugu, Nigeria - Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya amince da naɗin sababbin hadimai 101 da za su taimaka masa wajen gudanar da mulki.

Waɗanda gwamna Mbah ya nada sun haɗa da masu ba da shawara na musamman (SAs), manyan mataimaka na musamman (SSAs) da mataimaka na musamman (SAs).

Gwamna Peter Mbah.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Obi yana jagorantar zaman Majalisar zartarwa ta jiha Hoto: Peter Ndubuisi Mbah
Source: Twitter

Tribune Nigeria ta ce hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar (SSG), Farfesa Chidiebere Onyia, ya fitar ranar Litinin, inda ya ce naɗin ya fara aiki nan take.

Kara karanta wannan

Da gaske ne mataimakin gwamna ya ce a yi wa Tinubu ruwan duwatsu?

A cewar Onyia, mutum bakwai daga cikin waɗanda aka naɗa masu ba da shawara na musamman ne, shida manyan mataimaka na musamman, yayin da 88 kuma mataimaka na musamman ne.

Sunayen masu ba da shawara (SAs)

Masu ba da shawara na musamman da Gwamna Mbah ya nada sun haɗa da Dakta Fidelis Odo, mai kula da harkokin hulɗa da gwamnatoci da daidaita ayyuka da Mista Augustine Okoli, mai kula da harkokin manufofi da nazari.

Sai kuma Pedro Nwankwo wanda aka ba matsayin mai kula da hulɗa da masu ruwa da tsaki da harkokin al'umma da Chimezie Nkwuo, mai kula da bunƙasar tattalin arziki da Vitalis Okonkwo, mai kula da haɗa kan jama'a a matakin ƙananan hukumomi.

Sauran sune Mista Peter Omeje, mai kula da harkokin kasuwanci da bunƙasa kasuwanci; da Cif Sam Nwagu, mai kula da sasanta rikice-rikice da sulhu.

Sunayen manyan mataimaka (SSAs)

Manyan mataimaka na musamman sun haɗa da Rachael Okonkwo, mai kula da bunƙasa masana'antar fina-finai da ƙirƙire-ƙirƙire; Okey Ude, mai kula da hulɗa tsakanin jam'iyyu da wayar da kan jama'a; da Chinedu Chukwunwike, mai kula da sa ido kan harkokin jam'iyya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Sauran sun haɗa da Peter Ogbe, mai kula da bin ƙa'idojin doka da dokokin gudanarwa; Chinedu Ozoeluba, mai kula da sasanta rikicin iyaka da filaye; da Frank Udemezue, mai kula da bunƙasa ƙananan masana'antu da matsakaitan 'yan kasuwa.

Peter Mbah.
Gwamnan jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeirya, Peter Mbah Hoto: Peter Mbah
Source: Facebook

A rahoton Punch, sanarwar ta ce:

“An bai wa mataimaka na musamman nauyin da ya shafi kare dazuzzuka, tsaftar kasuwanni, kula da cibiyoyin kiwon lafiya, kare muhalli da bunƙasa al'umma.
“Daga cikin nauyin da aka ɗora wa SAs akwai hulɗa da matasa, wayar da kan mata, sadarwar jama'a, sa ido kan ababen more rayuwa, bunƙasa karkara, fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire da sauran ayyuka.”

Gwamnatin Enugu ta sa harajin kamfe

Kun ji cewa gwamnatin jihar Enugu ta bukaci jam'iyyun siyasa su biya Naira miliyan 150 kafin a ba su izinin yin tallace tallace na yakin neman zabe.

Hukumar ENSSAA ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen kare muhalli da kuma samar da kudaden shiga ga asusun jihar Enugu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262