Magana Ta Fito: Atiku Ya Bayyana Dalilin da Ya Sa Yake Son Dawo da Tallafin Fetur
- Atiku Abubakar ya ce bai yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma yana tambayar inda kudaden da aka samu daga cire shi suka tafi
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce kudaden ya kamata a yi amfani da su wajen rage talauci, inganta ilimi da samar da ayyukan yi
- Atiku ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a 2027, domin rage radadin da tattalin arziki ya jefa ‘yan Najeriya ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana dalilin da ya sa yake son dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2027.
Atiku ya ce bai yi adawa da matakin cire tallafin man fetur ba, sai dai ya ce har yanzu ‘yan Najeriya ba su ga yadda aka yi amfani da kudaden da aka samu bayan cire tallafin ba.

Source: Facebook
Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar BBC Hausa da aka wallafa ranar Juma’a, 28 ga watan Agustan 2026.
A yayin hirar an tambaye shi matakan da zai dauka domin taimakawa ‘yan Najeriya da ke fama da matsanancin tsadar rayuwa.
‘Ina kudin da aka samu?’
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ya ce gwamnatin yanzu ta cire tallafin man fetur, amma ba ta bayyana yadda aka yi amfani da kudaden da aka samu ba.
“Ban yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma ina kudin? Ina aka kai shi?” In ji shi.
A cewarsa, kudaden da aka samu ya kamata a karkatar da su wajen inganta rayuwar jama’a, musamman ta hanyar rage talauci da tallafawa harkar ilimi.
“An yi nufin rage talauci da taimaka wa yara su samu damar zuwa makaranta. Ina kudin yanzu?” in ji shi.
Ya ambaci Naira tiriliyan 30

Kara karanta wannan
Ba irin na baya ba ne"; Amaechi ya fayyace shirin Atiku na dawo da tallafin fetur
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma tambayi gwamnatin tarayya game da kudaden da ake cewa an samu sakamakon cire tallafin man fetur.
“Sun ce naira tiriliyan 30, ina kudin, me aka yi da shi?” Atiku ya tambaya.
Ya ce idan da an yi amfani da kudaden wajen ayyukan ci gaba, da yanayin rayuwar ‘yan Najeriya ya kasance daban.
Atiku ya bayyana cewa kudaden ya kamata a zuba su wajen magance matsalar tsaro, inganta ilimi, rage talauci da kuma samar da damarmaki ga matasa.
“Da sun yi amfani da kudin wajen samar da ci gaba, magance matsalolin tsaro, ilimi da samar da damarmaki ga matasa, da al’amura sun kasance daban,” in ji shi.
Atiku ya sake maganar tallafin man fetur
Atiku ya danganta bukatar dawo da tallafin man fetur da irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon tsadar kayan masarufi da karancin abinci.
Ya ce manufarsa ita ce tabbatar da cewa jama’a sun samu saukin rayuwa tare da amfani da albarkatun kasar wajen bunkasa tattalin arziki.
Dan siyasar ya kuma jaddada muhimmancin samar da ayyukan yi da damar dogaro da kai ga matasa.

Source: Facebook
Ya tuna cewa a zaben shugaban kasa na 2023, ya gabatar da shirin ware dala biliyan 10 domin bai wa matasa jari da za su fara sana’o’i da sauran harkokin kasuwanci.
Atiku ya ce samar da irin wadannan damarmaki na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen rage rashin aikin yi da kuma inganta rayuwar matasan Najeriya.
Atiku zai bude iyakokin Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya ce zai sake bude iyakokin Najeriya da kasashen makwabta idan aka zabe shi.
Atiku ya ce rufe iyakokin kasa ya kawo babban cikas ga kasuwancin da ake yi tsakanin Najeriya da kasashen makwabta tare da jefa matasa da dama cikin rashin aikin yi.
Asali: Legit.ng

