Ana Shirin Dauke Wuta a Najeriya bayan Sojoji Sun Lakada Jami'an Lantarki

Ana Shirin Dauke Wuta a Najeriya bayan Sojoji Sun Lakada Jami'an Lantarki

  • Kungiyar SSAEAC ta ba hukumomi wa'adin kwan uku domin daukar mataki kan zargin cin zarafin ma'aikatan wuta10 da sojojin sama suka yi
  • Kungiyar ta gargadi cewa za ta rufe dukkan harkar wutar lantarki a fadin Najeriya idan ba a warware batun ba kafin karewar wa'adin
  • Zargin ya biyo bayan katse wutar lantarki da ma'aikatan JED suka yi a rukunin gidajen sojojin sama sakamakon kin biyan kudin wuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi – Kungiyar manyan ma'aikatan harkar wutar lantarki (SSAEAC) ta bawa hukumomi wa'adin kwana uku domin magance zargin cin mutunci, duka, da tsare ma'aikatan wutar lantarki 10 da sojojin sama suka yi a jihar Bauchi.

Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa, Rilwanu Shehu, ya bayyana cewa ƙungiyar za ta rufe dukkanin harkar wutar lantarki a fadin ƙasar idan hukumomi suka gaza ɗaukar mataki kafin karewar wa'adin.

Kara karanta wannan

Da gaske ne mataimakin gwamna ya ce a yi wa Tinubu ruwan duwatsu?

Wajen da ke aikin wutar lantarki
Wajen da ake gyaran wutar lantarki. Hoto: TCN
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa Shehu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata zanga-zanga a jihar Bauchi biyo bayan farmakin da sojojin saman suka kai ofishin kamfanin rarraba wutar lantarki na Jos (JED) tare da kama ma'aikatansa.

Sojoji sun lakada jami'an JED

A cewar Shehu, sojojin saman sun afka ofishin JED ne a ranar 18 ga watan Satumba bayan ma'aikatan wutar lantarki sun yanke wutar rukunin gidajen sojojin sama da ke kan hanyar Ningi zuwa Kano sakamakon rashin biyan kuɗin wutar lantarki.

Shehu ya bayyana cewa kamfanin ya rigaya ya sanar da hukumomin sojojin saman kafin yanke wutar.

Ya ƙara da cewa:

"Muna cikin tsoro, ba ma tsira kuma ba za mu iya ci gaba da gudanar da ayyukanmu ba. Muna ba jami'an tsaro, 'yan sanda da DSS damar tsoma baki domin warware wannan al'amari ta hanyar lumana.
"Za mu tsaida harkokin masana'antar wutar lantarki a duk fadin kasar idan ba a dauki mataki kan jami'an NAF da suka ci mutuncin ma'aikatanmu ba."

Kara karanta wannan

Ana hurawa Tinubu wuta ya rage kudin litar man fetur zuwa N500

An tsare jami'an JED

Radio Najeriya ya ruwaito cewa sojojin saman sun tsare ma me ma'aikata 10 tare da tafiya da su zuwa wani wurin da ba a bayyana ba, inda a yanzu haka wasu daga cikinsu ke karɓar magani a asibiti sakamakon cin mutuncin da aka yi musu.

Wa'adin kwanaki ukun da ƙungiyar ta bayar ya fara ne daga ranar 21 zuwa 23 ga watan Satumba, 2026.

Shugaban ƙungiyar NUEE reshen jihar Bauchi, Sikamta Mshelinga, ya bukaci ma'aikata da su zauna a gida har sai an samu sabuwar umarni daga shugabanninsu na ƙasa.

Taswirar jihar Bauchi
Taswirar jihar Bauchi a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Dangote zai samar da wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa Aliko Dangote na shirin zuba jarin da ya wuce dala biliyan 10 a ɓangaren wutar lantarki domin taimakawa wajen magance karancin lantarki a nahiyar Afirka.

Aliko Dangote ya bayyana damuwarsa kan yadda mutane fiye da miliyan 600 a fadin nahiyar ke ci gaba da rayuwa ba tare da ingantacciyar wutar lantarki ba, inda ya jaddada cewa babu yadda za a samu ci gaba ba tare da lantarki ba.

Ya bayyana cewa wannan babban jari da yake shirin zubawa zai taimaka wajen gina muhimman masana'antu da hanyoyin da nahiyar ke buƙata domin samar da ayyukan yi da arziƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng