NDC da ADC Sun Ce za Su Kifar da Bola Tinubu a 2027 ko Babu Hadaka
- Jam’iyyar ADC ta ce ba ta buƙatar haɗa ƙarfi da sauran jam’iyyun adawa domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce ADC na da isasshen goyon bayan ‘yan Najeriya da zai ba ta damar cin zaɓen shugaban ƙasa
- A gefe guda, ƙungiyar OK Movement ta ƙi amincewa da haɗa kai, tana mai cewa hakan zai kawo cikas ga shirye-shiryen da ta saka a gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Jam’iyyar ADC, ta ce ba ta buƙatar haɗin gwiwar jam’iyyun adawa domin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana hakan yayin wata hira yayin da yake magana kan shirye-shiryen ADC na tunkarar zaɓen 2027.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa Bolaji Abdullahi ya ce duk da cewa ana ci gaba da tattaunawa tsakanin jam’iyyun adawa kan yiwuwar haɗin gwiwa a wasu fannoni, ADC ba ta dogara da irin wannan haɗin gwiwa domin samun nasara a zaɓen.
ADC tana da ƙarfin cin zaɓe
Bolaji Abdullahi ya ce tattaunawar haɗin gwiwar da aka fara tun farko an yi ta ne domin sauƙaƙa wa jam’iyyun adawa aikin samun nasara, amma ADC yanzu ta samu ƙarfin siyasar da za ta iya gudanar da yaƙin neman zaɓenta da kanta.
“Ba mu buƙatar haɗin gwiwa domin cin wannan zaɓe. ADC ba ta buƙatar haɗin gwiwa domin cin wannan zaɓe,”
In ji shi.
Ya ƙara da cewa jam’iyyun adawa na ci gaba da tattaunawa kan wasu hanyoyin haɗin gwiwa, musamman yadda za a kare ƙuri’un da aka kaɗa a lokacin zaɓen.
OK Movement ta ƙi haɗaka
A wani ɓangare kuma, ƙungiyar OK Movement da aka kafa domin tattara goyon baya ga haɗin tikitin Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta bayyana cewa ba za ta shiga wata ƙungiyar siyasa ta waje ko a haɗa ta da ita ba.
Ƙungiyar ta samu magoya baya daga Obidient Movement, Kwankwasiyya, NNPP da ADC, inda ta ce za ta ci gaba da kasancewa ƙungiya mai cin gashin kanta.
A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taron shugabanninta na ƙasa da aka gudanar a Abuja, ƙungiyar ta ce ba za ta amince da duk wani yunƙurin haɗa ta da wata ƙungiya da aka tsara daga waje ba.

Source: Facebook
Ta ce irin wannan mataki zai iya kawo cikas ga shirye-shiryen da ta riga ta fara, ya rikitar da asalin ƙungiyar da magoya bayanta suka sani, tare da lalata ƙoƙarin da aka yi wajen gina tasirinta.
'Tinubu na ‘yanayin firgici’
A wani labarin, mun ruwaito cewa ADC ta zargi Shugaba Bola Tinubu da shiga “yanayin firgici” sakamakon ƙarin tsadar rayuwa, musamman yadda gwamnati ta sake ƙoƙarin faɗaɗa amfani da motocin CNG.
Jam’iyyar ta ce matakin rage kuɗin sufuri ya zo shekaru uku a makare, domin gwamnati ta samu damar ɗaukar irin wannan mataki tun bayan cire tallafin man fetur da ya jawo tashin farashin sufuri.
ADC ta yi wannan martani ne bayan taron gaggawa tsakanin Shugaba Tinubu da gwamnonin jihohi kan hanyoyin rage farashin sufuri da sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya radadin tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng

