An Samu Jihar Farko da Ta Yarda da Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

An Samu Jihar Farko da Ta Yarda da Kafa 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

  • Majalisar Dokokin Jihar Osun ta zama ta farko a Najeriya da ta amince da kudirin sauya kundin tsarin mulki domin kafa rundunar ’yan sandan jihohi
  • Majalisar Dokokin Tarayya ta fayyace cewa kudirin kafa ’yan sandan jihohi ne kawai aka aika wa majalisun dokokin jihohi 36 domin su tattauna su amince
  • Majalisar Osun ta amince da kudirin ne gaba ɗaya bayan ’yan majalisar sun bayyana cewa kafa ’yan sandan jihohi zai taimaka wajen inganta tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun – Majalisar Dokokin Jihar Osun ta zama majalisar dokokin jiha ta farko da ta amince da kudirin sauya kundin tsarin mulkin Najeriya domin kafa rundunar ’yan sandan jihohi.

Matakin ya zo ne bayan Majalisar Dokokin Tarayya ta aika da kudirin zuwa majalisun dokokin jihohi 36 domin su yi nazari da kuma amincewa da shi.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa 7 sun shilla ƙasar Amurka, sun nemo abin da zai amfani 'yan Najeriya

Yan sandan jihohi
Dakarun rundunar 'yan sandan Najeriya. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Abin da aka aika wa jihohi

Punch ta wallafa cewa magatakardar Majalisar Dokokin Tarayya, Kamoru Ogunlana, ya ce kudirin kafa rundunar ’yan sandan jihohi ne kadai aka aika wa majalisun dokokin jihohi zuwa yanzu.

Ogunlana ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai taken “Majalisar Tarayya ta fayyace batun aika kudirin sauya kundin tsarin mulki ga majalisun dokokin jihohi.”

Ya ce a ranar 16 ga Satumba 2026, Majalisar Tarayya ta sanar da aika wa jihohi kudirin sauya kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.

A cewarsa, kudirin ya shafi kafa rundunar ’yan sandan jihohi da kuma wasu batutuwan da suka shafi hakan.

Osun za ta kafa ’yan sandan jiha

A zaman majalisar ranar Talata, Kakakin Majalisar Dokokin Osun, Adewale Egbedun, ya karanta wasikar Majalisar Tarayya da ke neman majalisun dokokin jihohi su tattauna tare da amincewa da kudirin.

Daga nan ne ’yan majalisar suka gudanar da muhawara kan kudirin, inda suka amince da shi baki daya.

Kara karanta wannan

Dangote ya waiwayi mata, ya yi masu tanadi na musamman a matatarsa

Ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Ife South, Lawrence Adeoti, da abokin aikinsa mai wakiltar Ede South, Taofeek Olayiwola, sun goyi bayan kudirin.

Taswirar jihar Osun
Taswirar jihar Osun a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Sun ce kafa rundunar ’yan sandan jihohi zai kara inganta tsaro a sassan Najeriya.

Dalilan goyon bayan kudirin

Adewumi Adeyemi, mai wakiltar Obokun, da Jeremiah Awoyeye, mai wakiltar Ife Central, su ma sun bayyana kudirin a matsayin wanda ya zo a lokacin da ya dace.

Sun ce kafa ’yan sandan jihohi zai karfafa tsarin tsaron kasar, musamman a matakin jihohi da kananan hukumomi.

Sun kuma ce hakan zai ba jihohi damar samar da jami’an tsaro da suka dace tare da mayar da martani cikin sauri ga matsalolin tsaro da suka taso a yankunansu.

Gargadi kan kai hari Osun

A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ta gargadi shugabannin Musulmi da Kirista a Jihar Osun kan wani rahoton shirin ’yan ta’adda na kai hare-hare a wuraren ibada.

An ruwaito cewa DSS ta gudanar da taruka daban-daban da al’ummar Musulmi da kungiyar CAN a Osogbo, inda ta shawarci shugabannin addinin da su dauki matakan kariya daga yiwuwar hare-haren.

Rahoton ya ce bayanan sirri sun nuna cewa ’yan ta’adda na shirin yada rashin tsaro zuwa kudancin Najeriya, musamman yankin Kudu maso Yamma, domin haifar da tashin hankali gabanin babban zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng