Trump Ya Tsokano Sojojin Iran, Sun Yi Barazanar kai Manyan Hare Hare
- Sojojin Iran sun yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na “halaka” Jamhuriyar Musulunci, suna mai cewa Iran a shirye take ta mayar da martani mai tsanani
- Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Iran ya zargi Trump da amfani da dandalin Majalisar Dinkin Duniya wajen neman ba da hujjar hare-haren da Amurka ke kaiwa Iran
- Sojojin Iran sun kuma yi gargadin cewa za su iya kai wa Amurka da Isra’ila hare-haren da suka fi na baya tsanani kuma ba za a iya hasashen irin martanin da za su mayar ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran – Sojojin Iran sun yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na “halaka” Jamhuriyar Musulunci, suna mai cewa irin kalaman na nuna abin da suka kira matsananciyar damuwa ta dabarun yaki da Amurka ke fuskanta.
Babban Hafsoshin Hafsoshin Sojin Iran ya zargi shugaban Amurkan da amfani da dandalin Majalisar Dinkin Duniya wajen neman ba da hujjar abin da ya kira “ta’addanci”.

Source: Getty Images
Iran ta yi wa Donald Trump martani
A cikin wata sanarwa da Mehr ta wallafa, rundunar sojin Iran ta ce kalaman Trump na nuna cewa Amurka ta shiga wani hali na rashin mafita a dabarunta na yakar Iran.
Ta ce maimaita barazanar Trump ba alamar karfin Amurka ba ce, sai dai abin da ta kira alamar matsananciyar damuwar dabarun yaki da kasar ke ciki.
Rundunar ta kuma gargadi Amurka da Isra’ila cewa dakarun Iran a shirye suke su kai musu hare-haren ramuwar gayya masu tsanani.
Ta ce hare-haren za su iya zama “masu murkushewa kuma marasa saukin hasashe” fiye da wadanda aka kai a farkon yakin.
Gargadin da Iran ta yi wa Amurka
Gidan talabijin na kasar Iran ya tabbatar da ganawar da aka yi tsakanin Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, da wakilin Amurka, Steve Witkoff.
An ce an gudanar da ganawar ne bisa bukatar bangaren Amurka, domin tattauna sharudan Iran da suka shafi sake bude mashigar ruwan Hormuz.

Kara karanta wannan
"Za a iya cikin kwanaki 7"; Iran ta sanar da Amurka sharadin bude mashigar Hormuz

Source: Getty Images
Al Jazeera ta wallafa cewa Majiyoyin diflomasiyya da na tsaro a Iran sun ce matsayin kasar da bukatunta ba su sauya ba.
Wata majiyar tsaro ta ce idan Amurka ta cika alkawuran da suka shafi bukatun Iran tare da samar da isassun tabbaci da garantin aiwatar da su, Iran na iya sassauta matsayinta domin ci gaba da tattaunawa.
A gefe guda, ana samun sakonni mabanbanta daga Tehran, inda wasu ke nuna shirin ci gaba da diflomasiyya yayin da rundunar sojin kasar ke gargadin cewa za ta kara karfin martani idan rikicin ya kara tsananta.
Trump ya sauya sunan AI
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce kalmar “Artificial Intelligence” wato basirar na’ura tana sa fasahar ta yi kama da abin da ba na gaskiya ba, inda ya ce ya fi son a kira ta “Super Intelligence”.
Trump ya bayyana hakan ne a wani dogon jawabi da ya yi a Majalisar Dinkin Duniya da ke New York ranar Talata, inda ya gabatar da kalmar “SI” a matsayin sabon suna ga fasahar.
Masana da suka yi magana sun ce akwai yiwuwar sabon sunan ba zai samu karbuwa sosai a masana’antar fasahar ba, yayin da Trump ya kuma bayyana cewa yana son a yi amfani da kalmar “super intelligence” a takardun gwamnatin Amurka.
Asali: Legit.ng
