Magana Ta Yi Nisa, 'Tinubu Must Go' Ta Raba Wasikun Hada kan Atiku, Obi da Sauransu

Magana Ta Yi Nisa, 'Tinubu Must Go' Ta Raba Wasikun Hada kan Atiku, Obi da Sauransu

  • TafiyarTinubu Must Go, TMG, ta nemi Atiku Abubakar, Peter Obi, Seyi Makinde da Omoyele Sowore su haɗa kai domin kayar da Bola Tinubu
  • TMG ta buƙaci ’yan siyasar su ajiye burinsu na kashin kansu gefe tare da shiga tattaunawar da za ta samar da ɗan takarar da zai wakilci ’yan adawa
  • Tafiyar ta ce haɗin kan ’yan adawa zai samar wa ’yan Najeriya damar kayar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shekarar 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – TafiyarTinubu Must Go, TMG, ta nemi Atiku Abubakar, Peter Obi, Gwamnan Oyo Seyi Makinde da Omoyele Sowore su haɗa kai domin samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda a zaɓen 2027.

TMG ta yi wannan kira ne a wata wasiƙa da ta aika wa ’yan siyasar huɗun, inda ta buƙace su da su ajiye muradun siyasa na kashin kansu gefe tare da shiga wata tattaunawa mai zurfi domin samar da ɗan takarar da zai fafata da Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya ta yi magana kan kama Atiku gabanin zaben 2027

Atiku Abubakar, Peter Obi da Bola Tinubu
Manyan 'yan takarar shugaban kasa 3 a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|Atiku Abubakar|Mr Peter Obi
Source: Twitter

Kokarin hada kan 'yan adawa

A sakon da Abba Hikima ya wallafa a Facebook, kungiyar ta ce kiran nata na daga cikin ƙoƙarin samar da haɗin kan ’yan adawa domin bai wa ’yan Najeriya damar sauya gwamnati.

A cikin wasiƙar da Abba Hikima ya sanya wa hannu, TMG ta ce tana wakiltar wani yunƙuri na ’yan ƙasa da ya haɗa ’yan Najeriya masu ra’ayoyin siyasa daban-daban domin cimma manufar haɗa kan ’yan adawa.

Ta ce:

“Babban buƙatarmu mai sauƙi shi ne manyan ’yan takarar adawa su gana, su tattauna cikin gaskiya, sannan su duba duk wata hanyar da za ta iya samar da ɗan takarar shugaban ƙasa guda da kowa ya amince da shi.”

Dalilan neman hadaka

TMG ta danganta kiranta da abin da ta bayyana a matsayin tabarbarewar tsaro da kuma matsalolin tattalin arziki da zamantakewa a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Ƙungiyar ta ambaci wani rahoton SBM Intelligence da ya ce an sace mutane 7,825 tare da kashe akalla 1,142 a Najeriya tsakanin Yuli 2025 zuwa Yuni 2026.

Kara karanta wannan

2027: Matasan Najeriya sun tafi Abuja domin hada Atiku da Obi su kwarfe Tinubu

Daily Nigerian ta wallafa cewa rahoton ya ƙara da cewa waɗanda aka sace da iyalansu sun biya Naira biliyan 7.78 a matsayin kuɗin fansa.

TMG ta kuma nuna damuwa kan hauhawar farashin kayayyaki, abinci da makamashi, kuɗin wutar lantarki da man fetur, rashin aikin yi da kuma raguwar ƙarfin sayen iyalai.

Omoyele Sowore a kotu
Dan takarar AAC, Omoyele Sowore a kotu. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Getty Images

TMG ta nemi Atiku, Obi, Makinde da Sowore su ci gaba da barin ƙofa a buɗe domin tattaunawa har zuwa lokacin zaɓe, tana mai cewa yanayin siyasa na iya sauyawa yayin da zaɓen 2027 ke gabatowa.

An nemi Obi ya janye takara

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Anambra ta ƙalubalanci Peter Obi da ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027, tana zarginsa da karya wasu manyan alkawuran da ya ɗauka.

A wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta tambayi lokacin da Obi zai janye daga takarar shugaban ƙasa, tana mai tuno da alkawarin da ya taɓa yi na yin hakan idan aka tabbatar da cewa ya bar Anambra da bashi.

Gwamnatin ta kuma ce Obi ya yi alkawarin yin murabus daga kujerar gwamna idan ma’aikata ba su samu albashi a kan lokaci ba, sannan ta yi zargin cewa ya karya waɗannan alkawura biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng