An fara kamfe amma NDC za ta yi fama da shari’a da ‘dan jam’iyya ya kai ta kotu

An fara kamfe amma NDC za ta yi fama da shari’a da ‘dan jam’iyya ya kai ta kotu

  • Pratt Tunde ya ce sauya sunansa da NDC ta yi, ya keta hakkinsa na zama dan takarar majalisar wakilai a Legas
  • ‘Dan siyasar ya yi gargadin cewa jinkirta shari'arsa da NDC na iya bata damarsa ta shiga zaben cikin lokaci
  • A lokacin da peter Obi ya soma kamfe, an ji lauyoyinsa sun jaddada cewa karar na da nufin kare zabin jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - ‘Dan kasuwa kuma ‘dan siyasa, Pratt Tunde, ya shigar da kara a kotu saboda an cire sunan shi a matsayin ‘dan takara a NDC.

Pratt Tunde ya yi ikirarin an sauya shi da wani ‘dan takara dabam wajen neman kujerar ‘dan majalisar wakilai na shiyyar Legas.

Peter Obi
'Yan takaran NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso tare da manyan jam'iyya a taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An yi karar NDC da INEC a kotu

Saboda haka ne ya shigar da kara a wata babbar kotun tarayya mai zama a garin Legas yana kalubalantar lamarin cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Zance ya ƙare, Peter Obi ya bayyana matsayarsa kan batun dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Pratt Tunde yana so kotu ta ce wannan mataki da jam’iyyar NDC ta dauka ya saba ka’ida kuma bai da gindin zama ta fuskar doka.

Lauyan ‘dan siyasar ya nemi a umarci INEC ta maida sunan shi a matsayin ‘dan takara.

Mai neman tikitin NDC ya ce ya ci zabe

Tunde ya ce da aka yi zaben tsaida gwani a karshen Mayun 2026, shi ne wanda ya samu nasara a gaban jami’an hukumar INEC.

Sai dai a cewarsa, daga baya shugabannin NDC sun canza shi da wani Tunji Sanni.

Lauyan Tunde ya ce maye gurbin sunan shi da Tunji Sanni da aka yi a boye ba daidai ba ne, don haka ya nemi kotu ta ceto takarar shi.

Tun da wannan sabanin kafin shiga zabe ne, lauyan ya ce sashe na 285 na kundin tsarin mulki ya bukaci a gaggauta shari’ar.

Ana sa ran kafin lokacin kwanaki 180 da aka yanke ya kure, alkali zai saurari karar.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Atiku ya fadi lokaci na karshe da zai yi takarar shugabancin Najeriya

Peter Obi
Peter Obi da Rabiu Kwankwaso wajen daukar 'yan takaran 2027 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

APC ta cinye komai a Ebonyi

An ji APC ta cinye dukkan mukaman kananan hukumomi a jihar Ebonyi a zaben da jam'iyyar PDP ta bayyana a matsayin tsagaron magudi.

Akwai Nweze Umahi, dan Minista David Umahi, wanda ya samu nasarar zama shugaban karamar hukumar Ohaozara yana 'dan shekara 28 a duniya.

PDP ta soki zaben, tana cewa an yi shi ne ba bisa tsarin mulki ba sannan gwamnatin jihar ba ta shirya gudanar da ingantaccen zabe ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng