Babbar Magana: Shugaban Kasa Ya Je har Amurka Ya Yi Raga Raga da Donald Trump
- Shugaban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva ya ce Shugaban Amurka Donald Trump ba shi da ikon mulkin ko tilasta wa sauran ƙasashe bin muradun Amurka
- Lula ya soki tsarin harajin Trump kan kayayyakin Brazil, yana mai cewa matakin ya shafi cinikayyar ƙasashen biyu
- Ya ce duk da raguwar ciniki da Amurka, Brazil ta ƙara cinikayya da China, Japan, Jamus da Tarayyar Turai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
New York, Amurka - Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya ragargaji shugaban kasar Amurka, Donald Trump.
Lula Silva ya ce Shugaban Amurka, Donald Trump, ba shi da ikon mulkin wasu ƙasashe ko tilasta musu bin abin da yake so.

Source: Getty Images
Lula ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da Christiane Amanpour ta tashar CNN, gabanin taron Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) da ke gudana a New York.

Kara karanta wannan
An ga tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe mataimakin kwamandan rundunar tsaro a Plateau
Lula ya soki tsarin Trump
Shugaban Brazil ya ce yadda Trump ke tafiyar da hulɗar ƙasa da ƙasa ya dogara ne kan tunanin cewa ƙasa mafi ƙarfi ce ya kamata ta tsara wa sauran ƙasashe yadda za su yi.
Lula ya ce an zabi Trump ne domin ya jagoranci Amurka, amma hakan bai ba shi damar mulkin wasu ƙasashe ba.
“Shugaba Trump an zaɓe shi ne ya zama shugaban Amurka. Yana da ikon mulkin Amurka, amma ba shi da ikon mulkin wasu ƙasashe,” in ji Lula.
Ya ƙara da cewa Trump ba shi da ikon tilasta wa wasu ƙasashe ra’ayinsa, yana mai cewa ya kamata ya kasance a shirye don tattaunawa da yin shawarwari.
Lula ya ce bai amince da tsarin da ƙasa ke cewa ita ce mafi ƙarfi, mafi arziki kuma mafi rinjaye, don haka dole sauran ƙasashe su yi biyayya ba.
‘Kowace ƙasa na da ikon cin gashin kanta’
Lula ya ce ya kamata kowace ƙasa ta samu damar kare ikon cin gashin kanta tare da bibiyar muradunta ba tare da tsoma bakin Amurka ba.
“Abin da muke son faɗa shi ne kowace ƙasa na da nata ikon cin gashin kanta. Suna kula da muradunsu, kuma Amurka ba za ta iya tilasta dokokinta ga sauran ƙasashe ba,” in ji shi.
Lula ya soki harajin Trump kan Brazil
Shugaban Brazil ya kuma soki harajin da gwamnatin Trump ta kakaba wa wasu kayayyakin da Brazil ke fitarwa zuwa Amurka.
A watan Yuli, Amurka ta sanya harajin kashi 25 cikin 100 kan wasu kayayyakin Brazil bayan wani bincike da Ofishin Wakilin Ciniki na Amurka (USTR) ya shafe shekara guda yana gudanarwa.
Sai dai Lula ya ce harajin ya samo asali ne daga “ƙarya”, yana mai cewa gwamnatinsa ta mayar da martani ta hanyar ƙarfafa alaƙar cinikayya da sauran ƙasashe.
Brazil ta ƙara ciniki da wasu ƙasashe
Lula ya ce fitar da kayayyakin Brazil zuwa Amurka ya ragu da kashi 9 cikin 100, yayin da shigo da kayayyaki daga Amurka zuwa Brazil ya ragu da kashi 8.5 cikin 100 bayan kakaba harajin.
A gefe guda, ya ce cinikayyar Brazil da China ta ƙaru da kashi 20 cikin 100. Ya ƙara da cewa cinikayyar Brazil da Japan ta ƙaru da kashi 18 cikin 100, yayin da ciniki da Jamus ya karu da kashi 60 cikin 100.
Lula ya kuma ce cinikayyar Brazil da Tarayyar Turai ta ƙaru da kashi 23 cikin 100.

Source: Getty Images
Trump ya sauya sunan fasahar AI
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Amurka, Donald Trump, ya sanar da sauya sunan fasahar Artificial Intelligence (AI)
Shugaba Trump ya bayyana cewa za a riƙa kiran fasahar Artificial Intelligence (AI) da “Super Intelligence” (SI), yana mai cewa sabon sunan ya fi bayyana ainihin fasahar.
Asali: Legit.ng

