An Yi Zaman Ƙeƙe da Ƙeƙe tsakanin Amurka da Iran, Trump Ya Magantu
- Shugaba Donald Trump ya ce jami’an Amurka da Iran sun gudanar da wani taro mai kyau a New York, yayin da rikicin kasashen biyu ya shiga wata na bakwai
- Wakilan Iran sun isa New York da izinin yin shawarwari, amma har yanzu ba a bayyana abin da aka tattauna a taron na tsawon sa’o’i uku ba
- Iran ta kuma bayyana sharudan da take bukata domin kawo karshen rikicin, ciki har da dakatar da hare-haren Amurka da takunkumi da kuma sakin kadarorinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa jami’an Amurka da Iran sun gudanar da wani “taro mai kyau” a New York ranar Talata, bayan jawabin da ya gabatar a Majalisar Dinkin Duniya.

Kara karanta wannan
Hakar ma’adanai: Atiku ya tausaya wa yaro, ya dauki dawainiyar karatunsa a makaranta
Taron ya gudana ne yayin da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya kai watanni bakwai, lamarin da ya haifar da tasiri kan farashin makamashi a duniya.

Source: Facebook
Amurka da Iran sun tattauna
Jerussalem Post ta wallafa cewa Trump ya ce yayin jawabin da ya yi a Majalisar Dinkin Duniya cewa har yanzu yana ganin akwai yiwuwar cimma yarjejeniya da Iran.
Ya yi tambaya kan ko Amurka za ta lalata Jamhuriyar Musulunci ta Iran gaba daya ko kuma ta nemi hanyar cimma yarjejeniya da ita.
Trump ya kuma ce yana ganin za a cimma yarjejeniya, yana mai alakanta hakan da lokacin da ya bayyana a matsayin bayan zabe.
Yawancin tawagar Iran sun fice daga zauren Majalisar Dinkin Duniya yayin da Trump ke gabatar da jawabin nasa.
Sai dai bayan wasu sa’o’i, wakilan kasashen biyu sun gudanar da ganawar da ta dauki tsawon sa’o’i uku.
Iran ta gindaya sharuda
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce Iran ta sanar da Amurka sharudan da take bukata domin kawo karshen rikicin ta hannun masu shiga tsakani daga Qatar.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Baghaei ya ce sharudan da tsarin tattaunawar ba sababbi ba ne, domin an riga an sanar da Amurka su tun farkon makon.
Ya ce matsayin Iran kan mashigar ruwan Hormuz da kuma tsaron yankin bai sauya ba, yana mai cewa halartar taron Majalisar Dinkin Duniya ya ba Iran damar bayyana matsayinta ga jami’an diflomasiyyar Amurka cikin karin bayani.
Batun kawo karshen hare-hare
Baghaei ya ce daga cikin sharudan Iran akwai kawo cikakken karshen hare-haren Amurka da killacewar ruwan teku da kuma takunkuman da aka kakaba mata.

Source: Getty Images
Ya kuma ce Iran na bukatar a saki kadarorinta da aka daskarar a matsayin wani bangare na matakan kawo karshen rikicin.
A nasa bangaren, Trump ya bayyana cewa Iran ba za ta taba samun makamin nukiliya ba, sannan ya bukaci a sake bude mashigar ruwan Hormuz gaba daya.
Ga bayanin Trump da Al Jazeera ta wallafa a X:
Jirgin Amurka ya fado
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Tsaron Australia, Richard Marles, ya ce wasu kayayyakin jirgin yakin F-35 sun karkata zuwa Hong Kong bisa kuskure.
Marles ya ce Australia ta samu labarin abin da ya faru, kuma tana aiki tare da Amurka da kamfanin Lockheed wajen taimakawa binciken lamarin.
Rahotanni sun ce kayan da aka shirya aikawa Amurka domin gyara sun karkata ne yayin da ake jigilar su daga Australia a lokacin bazara.
Asali: Legit.ng
