'Tinubu na cikin Firgici,' ADC Ta Ce Ta Tsorata Shugaban Najeriya kan 2027

'Tinubu na cikin Firgici,' ADC Ta Ce Ta Tsorata Shugaban Najeriya kan 2027

  • Jam’iyyar ADC ta ce shirin faɗaɗa amfani da motocin CNG domin rage farashin sufuri ya nuna cewa Shugaba Bola Tinubu ya shiga “yanayin firgici”
  • Ta bayyana matakin da gwamnati ta ɗauka a matsayin dabarar siyasa da ta zo shekaru uku a makare, musamman yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa
  • ADC ta ce gwamnatin Tinubu ta fara ɗaukar matakan rage kuɗin sufuri ne bayan ɗan takararta ya mayar da tallafin mai da tsadar rayuwa fagen siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC, ta ce sabon matakin gwamnatin tarayya na faɗaɗa amfani da motocin CNG domin rage farashin sufuri ya nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shiga “yanayin firgici” yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya bayyana mutanen da za su taka muhimmiyar rawa a tazarcen Tinubu

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani kan taron gaggawa da Shugaba Tinubu ya yi da gwamnonin jihohi ranar Juma’a domin tattauna hanyoyin rage tsadar sufuri a ƙasar.

Bola Tinubu da Bolaji Abdullahi
Shugaba Bola Tinubu a hagu da kakakin ADC, Bolaji Abdullahi a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Bolaji Abdullahi
Source: Facebook

Tribune ta wallafa cewa kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce matakin ba komai ba ne illa “dabarar siyasa” da ta zo shekaru uku a makare.

ADC ta soki shirin CNG

Jam’iyyar ta ce Shugaban Ƙasa da gwamnonin da wasa suke wajen rage farashin sufuri a faɗin ƙasar, suna mayar da martani ne ga tambayoyin da shirin ɗan takarar ADC, Atiku Abubakar, na samar da tallafi.

ADC ta tambayi dalilin da ya sa gwamnati ba ta sanya faɗaɗa amfani da motocin CNG cikin shirin farko na cire tallafin man fetur ba, idan har ta yi imanin cewa hakan zai taimaka wajen rage farashin sufuri.

Jam’iyyar ta ce:

“Sun bar mutane suna shan wahala tsawon shekaru uku, amma yanzu da zaɓe ya matso sai suka gano cewa za su iya rage farashin sufuri.”

Ta kuma tambayi dalilin da ya sa ba a gaggauta tura motocin CNG ba tun lokacin da ‘yan Najeriya suka fara fuskantar tsananin hauhawar kuɗin sufuri sakamakon cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

Tirkashi: APC ta dauka da zafi bayan Atiku ya yi wasu kalamai

Atiku Abubakar a wajen taro
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Paul O. Ibe
Source: Facebook

ADC ta danganta mataki da Atiku

ADC ta ce lokacin da gwamnati ta ɗauki matakin ya yi matuƙar bayyana, domin ya zo ne jim kaɗan bayan Atiku Abubakar ya mayar da batun tallafin mai da tsadar rayuwa cikin muhimman batutuwan siyasar ƙasa.

Leadership ta rahoto ya ce:

“Me ya sa sai da shirin tallafin Atiku ya sa wannan gwamnati ta fara rudewa da kuma fahimtar buƙatar rage farashin sufuri?”

Atiku zai sake buɗe iyakoki

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin sake buɗe sauran iyakokin ƙasar da aka rufe tare da sauƙaƙa shigo da zirga-zirgar kayayyaki.

Atiku, wanda ya taɓa zama mataimakin shugaban ƙasa, ya ce rufe iyakokin ƙasa ya tilasta wa wasu ‘yan kasuwa rufe sana’o’insu tare da taimakawa wajen ƙara ta’azzara matsalar tsaro a ƙasar.

Ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ADC da wasu mambobin jam’iyyar suka yaɗa a kafafen sada zumunta, inda ya ke magana da wasu mahalarta wani taro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng