'Matsala ne Dawo da Tallafin Mai': Malamin Musulunci Ya Gargaɗi Ƴan Siyasa kan Kamfe

'Matsala ne Dawo da Tallafin Mai': Malamin Musulunci Ya Gargaɗi Ƴan Siyasa kan Kamfe

  • Sheikh Haliru Maraya ya gargadi ‘yan siyasar da ke neman takara a 2027 da su guji yi wa ‘yan Najeriya alkawuran da ba za su iya cikawa ba
  • Malamin ya yi magana kan batun dawo da tallafin man fetur ba, domin hakan na iya kara jefa tattalin arzikin Najeriya cikin matsala mai tsanani
  • Maraya ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gyara matatun mai na kasar tare da gina sababbi domin rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Wani malamin addinin Musulunci kuma tsohon hadimin ga wasu tsofaffin gwamnonin Kaduna ya shawarci yan siyasa yayin kamfen.

Sheikh Haliru Maraya, ya gargadi ‘yan siyasar da ke neman mukamai a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Malamin Musulunci ya shawarci Tinubu, Atiku da Obi
Yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi. Hoto: Atiku Abubakar, Bayo Onanuga, Mr Peter Obi.
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a Kaduna ranar Lahadi, yayin da yake mayar da martani kan kiran da wasu ‘yan siyasa ke yi na a dawo da tallafin man fetur, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Akwai gagarumar matsala': Malamin addini ya bukaci Tinubu ya hakura da takara

Shawarar Sheikh Maraya ga ƴan siyasa

Maraya ya bukaci ‘yan takarar shugaban kasa da sauran ‘yan siyasa su kasance masu gaskiya ga ‘yan Najeriya game da halin da tattalin arzikin kasar yake ciki.

Ya ce ya kamata shugabanni su bayyana wa al’umma abubuwan da gwamnati za ta iya cimmawa cikin yanayi na gaskiya, maimakon yin alkawuran da ba za a iya cika su ba.

Malamin ya ce Najeriya ba za ta iya daukar nauyin dawo da tallafin man fetur ba ba tare da kara tsananta matsalar tattalin arzikin kasar ba.

Sheikh Maraya ya bukaci ‘yan siyasa su guji amfani da matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta wajen yin alkawuran da suka san ba za su iya cikawa ba.

Maraya ya ce halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki a yanzu ba zai iya daukar nauyin sake dawo da tsarin tallafin man fetur ba.

Ya ce:

“Ya kamata ‘yan takarar shugaban kasa su rika fada wa mutane gaskiya, ka da su yaudari ‘yan Najeriya saboda kawai suna son samun kuri’u. Allah ba ya son karya da yaudara."

Kara karanta wannan

Atiku zai bambanta da Tinubu, ya yi albishir ga matasa da ya gana da yan N Power

“A halin yanzu, a fadin gaskiya, tattalin arzikin Najeriya ba zai iya ci gaba da biyan tallafin man fetur kamar yadda aka yi a baya ba. Idan aka dawo da tallafin, tattalin arzikin zai iya durkushewa cikin kankanin lokaci, kuma gwamnati ta kasa gudanar da wasu muhimman ayyuka."
Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafin mai
Dan takarar shugaban ƙasa a ADC, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Getty Images

'Matsalar dawo da tallafin mai a Najeriya'

A cewar malamin, alkaluman da ake da su sun nuna cewa Najeriya na amfani da man fetur tsakanin lita miliyan 47 zuwa miliyan 64 a kullum.

Ya ce jimillar kudin lita guda, wanda ya hada da tacewa, sufuri, inshora da kudaden kwastam, ya kai kusan N1,218, cewar Tribune.

Maraya ya ce dawo da tallafin zai bukaci Gwamnatin Tarayya ta ware makudan kudade, wadanda da an yi amfani da su wajen samar da ababen more rayuwa da sauran ayyukan ci gaba.

Saboda haka, ya bukaci ‘yan siyasa su yi la’akari da illolin tattalin arziki kafin su gabatar wa masu kada kuri’a da alkawuran yakin neman zabe.

Maraya ya ce Najeriya na bukatar shugabannin da za su kasance masu karfin hali wajen fada wa ‘yan kasa gaskiya game da halin tattalin arzikin kasar.

Kamfe: DSS za ta ba Atiku, Obi tsaro

Mun ba ku labarin cewa Hukumar DSS ta ƙara tsaurara matakan tsaro ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Ritimi Amaechi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Atiku ya bayyana dalilin da ya sa yake son dawo da tallafin fetur

Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin kare dukkan ’yan takarar shugaban ƙasa 18 da mataimakansu.

INEC ta wallafa sunayen ’yan takarar gwamna da majalisun jihohi na 2027, yayin da wasu fitattun ’yan siyasa suka ɓace daga jerin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.