Ma'aikacin Zabe Zai Iya Amsar Kyauta Daga Hannun Agents na Jam'iyyu, Dr Jamil Zarewa

Ma'aikacin Zabe Zai Iya Amsar Kyauta Daga Hannun Agents na Jam'iyyu, Dr Jamil Zarewa

Ranar Asabar, 18 ga watan Maris za'a gudanar da zaben gwamnonin Najeriya da yan majalisun jiha a fadin jihohi 28.

Rahotanni sun gabata kan yadda wasu wakilan jam'iyyu ke yiwa ma'aikatan wucin gadi da hukumar zabe INEC ta dauka kyaututtuka ranar zabe.

A wasu wuraren, har abincin karin kumallo wadannan wakilan ke musu kafin su kama aikin zaben.

Shehin Malamin addinin Musulunci kuma lakcara a tsangayar nazarin addinin Musulunci ta jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria, Dakta Jamilu Zarewa, ya yi tsokaci kan wannan lamari.

Ya amsa tambaya kan hukuncin kudin da jam'iyyu ke ba malaman zabe a lokacin zabe.

Zarewa
Dr Jamil Zarewa ya bada amsa kan tambaya Hoto: Abu Uwaimir TV
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ga yadda tambayar ta kasance da amsa:

Tambaya

Kara karanta wannan

Zabo Tinubu ya ba mutane da yawa mamaki, Garba Shehu ya yi magana mai daukar hankali

Assalamualaikum, Malam meye hukuncin kudin da jam'iyyu ke ba malaman zabe a lokacin zabe ? alhali su malaman zaben hukumar zabe za ta biya su kudin aikinsu?

To malam kasan kowa da account number din shi a wurinsu, jiya bayan na dawo gida sai aka min alert na kudin rumfar !

Amsa

Wa alaikum assalam,

Wannan kudin da kuke amsa haramun ne kuma cin hanci ne, saboda an ba ka ne saboda kujerarka ta ma'aikacin zabe, inda a gidanku kake da ba su ba ka ba.

Annabi S.A.W. yana cewa a cikin hadisin da Abu-dawud ya rawaito "Duk wanda muka sanya shi wani aiki sannan muka yanka masa albashi akan aikin, to duk abin da ya karba bayan haka wuta bal-bal ya ci".

Annabi S.A.W. ya fusata sosai kuma ya yi maganganu masu kaushi lokacin da ya aika IBNU-ALLUTBIYYA karbo zakka amma kuma sai aka ba shi kyauta ya karbe kamar yadda Bukhari da Muslim suka rawaito.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban APC Na Kasa Ya Fasa Kwai, Ya Ce Zaben Shugaban Kasa Yana da Naƙasu

Hadisan da suka gabata suna nuna cewa: haramun ne ma'aikacin da yake da albashi ko alawus ya amshi kyautar da aka yi masa saboda aikinsa, in har ya amsa kuma to ya ci wuta rashawa.

Idan ma'akaicin zabe ya karbi kyauta daga jam'iyyu, magudin zabe ba zai yi wahala ba, daga cikin salon magana a harshen Hausa "Duk Wanda ya mika hannu ba zai iya mike kafa ba" wannan yasa Musulunci ya haramta irin wannan Ihsanin.

Allah ne mafi sani.

Dr Jamilu Yusuf Zarewa

17/03/2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel