Da Gaske Hukumar Hisbah Ta Hana Kiristoci Gudanar da Ibada a Sokoto?
- Hukumar Hisbah ta yi magana kan zargin hana Kiristoci gudanar da ibadarsu, wanda ya jawo maganganu a jihar
- Kwamandan hukumar, Dakta Usman Abdullahi Jatau, ya ce dokar kafa Hisbah ta shafi Musulmi ne kawai, ba ta da ikon tsara addinin Kirista
- Jatau ya bukaci jama’a su yi watsi da bayanan da ba su da tushe, domin kauce wa rikicin addini tare da tabbatar da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta yi martani kan rahotannin da ke cewa ta sanya dokoki domin takaita yadda Kiristoci ke gudanar da ibada.
Wannan martanin ya biyo bayan wasu zarge-zarge da suka bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ce hukumar na tsoma baki cikin harkokin addini.

Source: Original
Kwamandan hukumar Hisbah ta Sokoto, Dakta Usman Abdullahi Jatau, ya bayyana zarge-zargen a matsayin karya da yaudara, cewar Punch.
Jatau ya ce irin wadannan ikirari na iya haddasa rikicin addini da kawo rashin fahimta tsakanin al’ummomin jihar.
Ya bayyana cewa zargin ya samo asali ne daga wani da ya yi rubutu mai suna @radical.okoja.bia da wasu mutane.
An yi ikirarin cewa an hana haduwar maza da mata a majami’u, sannan ana bukatar rabuwar maza da mata yayin ibada.
Haka kuma, an yi zargin cewa fastoci ba za su zauna tare da matansu a lokacin ibada ba.
Wasu bayanan sun nuna cewa wai wadannan matakai wani shiri ne na mayar da Najeriya kasar Musulunci daga Sokoto.
Sai dai Jatau ya yi watsi da wadannan zarge-zarge, inda ya ce dokar kafa Hisbah ta Sokoto ta shafi Musulmi ne kawai.
Ya ce hukumar ba ta da ikon tsara yadda Kiristoci za su gudanar da ibadarsu ko yadda za su gudanar da tarurrukansu.
Kwamandan ya ce danganta irin wadannan takunkumi da hukumar Hisbah karkatar da gaskiya ne da zai iya lalata zaman lafiya.
Ya bayyana cewa manufar martaninsu ita ce gyara kura-kuran bayanai da kuma bambance gaskiya daga zarge-zargen da ba su da tushe.
Jatau ya kuma gargadi jama’a kan alakanta hukumar da batutuwan siyasa ko zargin wani shiri na Musuluntar da Najeriya.
Ya ce irin wadannan ikirari ba su da alaka da nauyin da doka ta dora wa hukumar Hisbah.
Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya su guji yada bayanan da ba a tantance ba, domin kare zaman lafiya da mutunta juna.
Ya ce irin wadannan ikirari ba su da alaka da nauyin da doka ta dora wa hukumar Hisbah.
Hukumar ta bukaci ‘yan Najeriya su guji yada bayanan da ba a tantance ba, domin kare zaman lafiya da mutunta juna.
Magidanci ya zargi Kwamishinan Hisbah da cin amana
An ji cewa wani magidanci ya zargi Kwamishinan Hisbah na dindindin a Zamfara da amfani da matsayinsa wajen tilasta rabuwar aurensa.
Mai ƙarar ya ce Kwamishinan, Faruk Dandalin Faila, daga baya ya auri tsohuwar matarsa Aisha bayan an raba aurensu.
Ya kuma nemi gwamnatin Zamfara ta gudanar da bincike da kuma yadda ’ya’yansa biyu suka shiga hannun Sirajo Kwaren Ganuwa.
Asali: Legit.ng

