Tambayoyi 7 da ke Bukatar Amsa Kafin Sanin Hallacin Mining Inji Sheikh Zarewa

Tambayoyi 7 da ke Bukatar Amsa Kafin Sanin Hallacin Mining Inji Sheikh Zarewa

  • Mutane sun bijirowa Jamilu Yusuf Zarewa tambayoyi game da hukuncin yin mining da sauran harkokin Crypto a musulunci
  • Malamin ya ce ba zai iya amsa tambayar ba domin har yanzu bai gama bincike ba tukuna, yana jiran amsoshin wasu batutuwa
  • Daga cikin abubuwan da Sheikh Jamilu Yusuf Zarewa zai so sani har da yadda ake samun kudi da tsarin da yadda ake ba da lada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - An jefawa Sheikh Jamilu Yusuf Zarewa tambayoyi game da hukuncin yin mining a mahangar addinin musulunci.

An yi wa malamin fikihun musuluncin tambaya ne ganin yadda wannan aiki na mining ya zama ruwan dare a kwanakin nan.

'Yan Mining
Sheikh Jamilu Zarewaya dakata wajen yin fatawa a kan Mining da Crpto Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jamilu Yusuf Zarewa ya dawo karatu

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ɗauki zafi, ya ba da umarnin a kama tsohon Sarkin Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta fahimci cewa an bijiro da tambayar ne wajen karatun littafin Muqaddimatul Iziyyah da aka yi ranar Alhamis.

A makon nan Jamilu Yusuf Zarewa ya dawo da yin karatun fikihun a babban masallacin da ke jami’ar Ahmadu Bello a Zariya.

Crypto: An yi tambaya a kan Mining

Amma shehin malamin bai ba da amsa ba tukuna, ya jero wasu tambayoyi da ya ce zai bukaci sanin amsarsu tukuna.

Idan Jamilu Yusuf Zarewa ya fahimci mas’alar da kyau, wannan zai ba shi damar yin fatawa a kan hallaci ko haramci.

Da zarar masana harkar Crypto da mining sun yi wa malamin karin haske, zai yi bayanin fahimtarsa a mahangar musulunci.

Zarewa ya aikawa 'Yan Mining tambayoyi

Daga cikin tambayoyin, malamin ya bukaci sanin yadda latse-latsen da ake yi ta waya yake rikida ya zama kudi a zahiri.

Kara karanta wannan

Sabon sarki: Matasa sun yi a zanga zanga, sun nemi Tinubu ya takawa Abba birki

Da alama malamin yana tsoron ‘mining’ ya yi kama da caca wanda ya haramta a addini.

1. An ce mining danne-danne za ka yi ta yi a waya, har su zama coins, ta yaya wadannan danne-danne suke rikidewa su zama kudi?

2. Shin yawan danne-dannenka shi ne yawan point/Coins din da za ka samu, ko Kuma canki in canka ne?

3. Wadanne hanyoyi ne Sharia ta yarda da su wajan samun kudi da Kuma mallakar abu?

4. Wadanne hikimomi ne suka sanya Allah Ya haramta caca?

5. Tun da Mining ba kudi ake sanyawa ba, ta wadanne hanyoyi kamfaninnikan da suke kula da mining suke samun kudin da za su rabawa membars/Costomominsu, idan lokacin fashewar abin ya yi?

6. Shin idan aka cuceka kana da hakkin ka bi kadin hakkinka, Kuma Ina za ka je in ka tashi kai kara?

7. Shin Mining GAME ne ko kuma nema ne da jibin-goshi?

Malamin ya karasa da cewa:

Kara karanta wannan

"Wannan ba cigaba ba ne': Hadimin Buhari ya caccaki Majalisa kan rusa masarautun Kano

"WANDA YA SANI YA TAIMAKA MANA DA AMSAR TAMBAYOYIN NAN !"

- Jamilu Yusuf Zarewa

Limami ya ja hankali kan Mining

A hudubarsa a masallacin ITN, Dr. Sa’ad Abubakar ya yi tsokaci a kan wannan sabon salon neman kudi da ya rudi mutanen Najeriya.

Limamin bai bayyana hukuncin mining a musulunci ba, sai dai ya ce mutane sun shiga rudani saboda yadda ra’ayin malamai ya rabu a kai.

Tashi da saukar Naira a kan Dala

Kwanaki bayan aka ji labari Naira ta yi ta tashi har ana murna, yanzu Dalar kasar Amurkan ta koma sukuwa a kan kudin Najeriya.

Tun can wasu masana sun ce babu tabbas a kan irin tashin da Naira ta yi, a yau an koma gidan jiya, kaya na neman sake yin tsada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel