Magana Ta Girma: An Tura Fitacciyar Yar TikTok Gidan Yari kan Zagin Wani Dan Siyasa a Kano
- Kotu ta ba da umarnin a tsare Khadija Muhammad Yar Lele a gidan gyaran hali da ke Kano kan zargin bata sunan wani dan siyasa da kuma zaginsa
- Bayanai sun nuna cewa an gurfanar da matashiyar, wacce ta dhahara a TikTok a gaban babbar kotun Shari’a da ke Post Office, Kano Municipal
- Kotun ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa 14 ga Oktoba, 2026 bayan sauraron kowane bangare a zaman da ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Wata fitacciyar mai amfani da kafar sada zumunta ta TikTok, Khadija Muhammad Yar Lele, ta shiga hannun hukumar gyaran hali a Kano.
An tura yar TikTok din gidan gyaran hali ne kan zargin bata suna da kuma yi wa wani dan siyasa cin mutunci bayan gurfanarda ita a gaban kotu.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Source: Facebook
An gurfanar da Khadija Yarlele a kotu
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an gurfanar da Khadija a gaban babbar kotun Shari’a da ke Post Office, karamar hukumar Kano Municipal, karkashin jagorancin Mai Shari’a Garba Malafa
Rahotanni sun nuna cewa ‘yan sanda ne suka shigar da karar da ake tuhumarta da aikata laifuffukan, wanda ya kunshi taba mutunci da zagin dan siyasa a Kano.
Bayan karanta mata tuhume-tuhumen, wadda ake tuhuma ta musanta dukkan zarge-zargen da ake yi mata.
Kotu ta tura yar TikTok gidan yari
Lauyan masu gabatar da kara, Barrista Awaisu Sani Lawan, ya bukaci kotun da ta dage sauraron karar domin ba wa bangaren masu gabatar da kara damar gabatar da shaidu a zaman da za a yi na gaba.
Bayan sauraron bangarorin biyu, kotun ta bayar da umarnin tsare Khadija a gidan gyaran hali, sannan ta dage ci gaba da sauraron karar zuwa 14 ga Oktoba, 2026, domin sake gurfanar da ita da ci gaba da shari’ar.
Wane zargi ake yi wa yar TikTok din?
A baya dai an zargi wadda ake tuhumar da wallafa wani bidiyo a shafinta na TikTok, inda ake zargin ta yi kalaman batanci ga mai shigar da kara, wanda aka bayyana da suna MD Hassan, cewar rahoton Freedom Radio.

Source: Getty Images
Bayanan da aka tattaro sun nuna cewa MD Hassan, wani fitaccen dan siyasa ne a yankin karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano.
A cikin bidiyon, ana zargin an ji yar TikTok din tana kiran dan siyasar da “dan karuwa”, kalmar da ta kai ga gurfanar da ita a gaban kotun shari'a domin daukar matakin doka.
Hisbah ta cafke dan TikTok a Kano
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar Hisbah ta Kano ta kama fitaccen 'dan TikTok, Namadina Tudunwada kan zargin yada sakonnin da ke karfafa zina.
Mataimakin Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Kano, Mujahid Aminuddeen, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ana zargin ya kwatanta kudin aure da na zina a wani bidiyo da ya wallafa, wanda Hisbah ta ce kalamansa na iya jawo matasa su guji aure, su rungumi zina a jihar.
Asali: Legit.ng
