Magoya Bayan Kwankwaso Sun Fusata, Sun Fara Nuna wa Gwamna Abba Yatsa a Kano
- Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf da takalar ’yan adawa yayin da ake tunkarar zaben 2027
- Kungiyar magoya bayan Sanata Rabiu Kwankwaso ta ce ana dakile ’yan majalisa masu adawa da gwamnati tare da hana su ayyuka
- Kungiyar Kwankwasiyya ta kuma soki kalaman da ta danganta ga Antoni Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a a wani shirin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Kungiyar Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamma Abba Kabir Yusuf da muzgunawa yan adawa.
Magoya bayan dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC, Rabiu Kwankwaso sun kuma zargi gwamnatin Abba da hana yan Majalisar jam'iyyun adawa gudanar da ayyukansu.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin yan Kwankwasiyya, Dr Habib Mai Lemo, ya fitar.

Kara karanta wannan
Sokoto: Sunayen malamai da za su tantance kalaman Sheikh Musa Lukuwa kan Annabi SAW
Kwankwasiyya ta dura kan gwamnatin Kano
Ta yi zargin cewa dakatar da wasu kansiloli, yunƙurin dakatarwa ko sauya wurin wasu ayyukan mazabu na tarayya da kuma barazanar da ake yi wa masu sharhi kan harkokin siyasa na daga cikin wani sabon salo na tsoratar da ’yan adawa a jihar.
Mai Lemo ya ambaci wasiƙar da ake zargin Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Kano ta fitar, inda ta nemi a dakatar da wani aikin gina hanya na mazabar tarayya ta Ungogo/Minjibir. tare da sauya wurinsa.
Ya ƙalubalanci gwamnatin jihar da ta bayyana dalilin da ya sa ayyukan da ’yan majalisar adawa suka samar wa al’umma suke fuskantar abin da ya kira “tsoma bakin hukuma ”
“Bai kamata a hana mutane hanya, makaranta, cibiyar kiwon lafiya ko wani aiki na jama’a ba saboda kawai wakilin da aka zaɓa wanda ya samar da aikin ɗan jam’iyyar adawa ne,” in ji shi.
Batun dakatar da kansiloli a Kano
Dangane da rahotannin dakatar da kansiloli, Kwankwasiyya ta ce an dakatar da kansiloli uku a ƙaramar hukumar Kano Municipal kan zarge-zargen da suka shafi aiwatar da ayyukan raya ƙasa.
Ta kuma yi zargin cewa an dakatar da kansiloli biyu a ƙaramar hukumar Tarauni saboda ci gaba da alaƙarsu da yan Kwankwasiyya.
Mai Lemo ya yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kuma a bayyane kan dakatarwar, ciki har da zarge-zargen da ake yi wa kansilolin da abin ya shafa da kuma hujjojin da hukumomi suka dogara da su.
Ya jaddada cewa kasancewa cikin wata jam’iyyar siyasa ba laifi ba ne, kuma bai kamata a dakatar da zaɓaɓɓun wakilai ko a gallaza musu ta fuskar gudanarwa saboda sun ƙi sauya sheka ba.
Barazana ga masu sharhi kan siyasa
Kungiyar Kwankwasiyya ta kuma soki kalaman da ta danganta ga Antoni Janar na Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a a wani shirin siyasa.

Source: Facebook
Ta yi zargin cewa ya yi barazanar kama masu sharhi kan siyasa, ’yan adawa da magoya bayan Kwankwasiyya da ke sukar gwamnati a rediyo da kafafen sada zumunta.
Kungiyar ta ce za ta ci gaba da zama cikin lumana da bin doka yayin da take kare dimokuraɗiyya da muradun mambobinta.
Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, gwamnatin Kano ba ta mayar da martani kan zarge-zargen ba.
Kwankwasiyya ce ta kai Abba kan mulki
Kun ji cewa jam'iyyar adawa ta NDC ta ce ba ta da fargabar tunkarar babban zaɓen 2027 a Kano duk da APC ke mulki a sama da kasa.
Mai magana da yawun jam'iyyar a Kano, Yusuf Fasaha, ya shaida wa Legit cewa tun da farko gwamnatin Kano ta samu nasarar lashe zaɓe ne sakamakon ƙarfin tafiyar Kwankwasiyya.
Asali: Legit.ng

