2027: Umarnin da Tinubu Ya ba DSS kan Atiku, Obi, Kwankwaso da Sauransu
- Hukumar DSS ta ƙara tsaurara matakan tsaro ga Atiku Abubakar, Peter Obi, Ritimi Amaechi da Rabiu Musa Kwankwaso
- Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin kare dukkan ’yan takarar shugaban ƙasa 18 da mataimakansu
- INEC ta wallafa sunayen ’yan takarar gwamna da majalisun jihohi na 2027, yayin da wasu fitattun ’yan siyasa suka ɓace daga jerin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin kare ’yan takarar shugaban kasa gabanin fara kamfen.
Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta ƙara tsaurara tsaro ga Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ’yan takarar shugaban ƙasa 16.

Source: Twitter
Hakan na zuwa ne yayin da ’yan takarar ke shirin shiga filin kamfen gabanin zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a watan Janairun 2027, cewar Punch.
Haka kuma, an faɗaɗa wannan tsarin tsaro ga dukkan ’yan takarar mataimakin shugaban ƙasa, ciki har da tsohon gwamna Rotimi Amaechi.
Amaechi na takarar mataimakin shugaban ƙasa ne a jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, tare da Atiku Abubakar.
Haka kuma, Rabiu Musa Kwankwaso ne ke neman kujerar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar Nigeria Democratic Congress, NDC, tare da Peter Obi.
Majiyoyi sun shaida wa The Nation cewa dukkan ’yan takarar gwamna da mataimakansu ma suna cikin tsarin tsaron da aka ƙara.
Haka kuma, ’yan takarar Majalisar Ƙasa da na Majalisun Jihohi a wuraren da ake ganin za su iya zama wuraren rikici suna ƙarƙashin kulawa ta musamman.
Wannan bayani ya fito ne a ranar da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta wallafa jerin sunayen dukkan ’yan takarar gwamna da Majalisar Jiha.
An gano cewa matakin hukumar DSS ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na bai wa dukkan ’yan takara 18 kariya mai ƙarfi.
Majiyar ta ce Tinubu na son a gudanar da zaɓen cikin ’yanci da adalci, ba tare da nuna fifiko ga kowanne ɗan takara ba.
Baya ga Tinubu, wanda yake ɗan takarar jam’iyyar APC, Atiku da Obi, akwai wasu ’yan takara da dama da za su fafata a zaɓen.
Daga cikinsu akwai Sanata Sandy Onor na PDP, Omoyele Sowore na AAC, Donald Duke na PRP da Okwori Adam Elizabeth Frederick na NDP.
Sauran sun haɗa da Chukwu Anita Zugwai na YPP, Rufai Adekunle Omoaje na AA, Adenuga Sunday na BP da Memeh Samuel na DLA.

Source: Facebook
Yan takarar mataimakan shugaban kasa a Najeriya
A cikin ’yan takarar mataimakan shugaban ƙasa akwai Rabi'u Kwankwaso na NDC, Rotimi Amaechi na ADC, Shehu Hussaini na AA, Egbeola Olawale Mertins na YPP, Ike Chinazam na ADP da Kashim Shettima na APC.
Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin samar da kariya ba tare da nuna bambanci ba ga dukkan ’yan takara, cewar Tribune.
“Dukkan ’yan takara ana kula da su. DSS na tura isassun jami’ai domin gudanar da ayyukan kare lafiyar ’yan takara."
- In ji majiyar
Majiyar ta ce dukkan ’yan takarar gwamna da mataimakansu ma suna samun kariya daga DSS domin gudanar da kamfen cikin kwanciyar hankali.
Ta ce babban burin matakin shi ne tabbatar da cewa kowa ya samu damar yin kamfen cikin ’yanci da kuma gudanar da zaɓe ba tare da matsala ba.
Majiyar ta ce an gano wasu jihohin da ake ganin za su iya zama wuraren rikici, inda aka sanya ido na musamman kan ayyukan siyasa.
Waɗanda za su jagoranci kamfen ɗin Tinubu
An ji cewa Shugaban Bola Tinubu ne shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaɓen APC na 2027, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ke cikin tafiyar.
An naɗa tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta Janar na kwamitin, yayin da Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama sakataren kwamitin.
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin a wata sanarwa.
Asali: Legit.ng


