"Najeriya Ta Yi Rashi," Ododo Ya Yi Alhini da Aka Tabbatar da Rasuwar Tsohon Gwamna a Najeriya

"Najeriya Ta Yi Rashi," Ododo Ya Yi Alhini da Aka Tabbatar da Rasuwar Tsohon Gwamna a Najeriya

  • Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar tsohon gwamna, Alhaji Ibrahim Idris, yana da shekaru 77 a wani asibiti da ke Birtaniya
  • Gwamna Ahmed Usman Ododo ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku tare da sanar da jana’izar gwamnati ga marigayin
  • Idris ya shugabanci jihar Kogi daga 2003 zuwa 2012, inda ya kasance gwamnan da ya fi dadewa a kan mulki a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi, Nigeria - Gwamnatin jihar Kogi ta tabbatar da rasuwar tsohon gwamna, Alhaji Ibrahim Idris a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa, Kingsley Fanwo, ya fitar.

A cikin sanarwar, Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana matukar alhininsa kan rasuwar tsohon gwamnan, yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne ga jihar Kogi da Najeriya baki daya.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon gwamna a Najeriya, Alhaji Ibrahim Idris ya rasu

Ododo.
Gwamna jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo a fadar gwamnati da ke Lokoja Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Ododo, wanda aka ruwaito ya ziyarci gidan marigayin da ke Abuja, ya jajanta wa iyalansa.

Gwamna Ododo ya yi alhinin rashin Idris

Gwamnan ya bayyana cewa jihar Kogi ta yi rashin wani fitaccen dan ta wanda ya sadaukar da wani bangane mai yawa na rayuwarsa wajen yi wa jama’a hidima.

Ododo ya ayyana jana’izar gwamnati ga tsohon gwamnan, inda ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin dukkan kudaden jana’izarsa tare da shirya masa jana’izar da ta dace da matsayinsa.

Ododo ya ayyana makokin kwanaki 3

Gwamnan ya kuma ayyana zaman makoki na kwanaki uku domin girmama marigayin, sannan ya bayar da umarnin sauke tutar Najeriya da ta jihar Kogi zuwa rabi a dukkan ofisoshin gwamnati da cibiyoyi a tsawon lokacin.

A cewar gwamnan, gwamnatin marigayi Idris ta aiwatar da muhimman ayyuka a fannonin gine-gine, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman bangarori, yana mai cewa tasirinsa zai ci gaba da kasancewa cikin tarihin ci gaban jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi? Gwamna ya tsige kwamishina, ya kore shi daga aiki nan take

“Baya ga ayyuka da manufofin da ake dangantawa da gwamnatinsa, za a tuna da Alhaji Ibrahim Idris a matsayin ma’aikacin gwamnati wanda ya sadaukar da kansa wajen sauke nauyin da jama’a suka dora masa.
“Zaman da ya yi a mukaman gwamnati ya kasance wani muhimmin babi a tafiyar siyasa da ci gaban jihar Kogi.
“Madadin Gwamnatin Jihar Kogi da al’ummarta, Gwamna Ahmed Usman Ododo ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan Idris, abokansa, abokan aikinsa da duk wadanda ke alhinin rasuwar tsohon gwamnan."

- Gwamna Ahmed Ododo.

Ibrahim Idris.
Tsohon gwamnan jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya, Alhaji Ibrahim Idris
Source: Facebook

Takaitaccen tarihin Ibrahim Idris

Marigayi Idris ya kasance gwamnan jihar daga 2003 zuwa 2012. Ya kama aiki a ranar 29 ga Mayu, 2003, bayan ya lashe zaben gwamna a karkashin jam’iyyar PDP.

Bayan Kotun Zaben Gwamna ta soke nasarar da ya samu a zaben 2007, Idris ya koma kan mulki bayan ya sake lashe zaben da aka gudanar a ranar 29 ga Maris, 2008, inda ya ci gaba da mulki har zuwa watan Janairun 2012.

Ya shafe kusan shekaru tara yana mulkin jihar Kogi, lamarin da ya sa ya zama gwamnan da ya fi kowa dadewa a kan mulkin jihar zuwa yanzu, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Sanata Yari na jagorantar kamfen din Tinubu, ya yi babban rashi a rayuwa

Tsohon shugaban PDP ya kwanta dama

Kun ji cewa tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Alhaji Bamanga Tukur, ya rasu yana da shekara 91 bayan fama da rashin lafiya.

Bamanga Tukur ya taɓa zama gwamnan tsohuwar Jihar Gongola tare da riƙe muƙaman gwamnati da na siyasa daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262