Yadda Mutanen Tinubu Suka Zagaya kan Malaman Izala da Darika a Najeriya

Yadda Mutanen Tinubu Suka Zagaya kan Malaman Izala da Darika a Najeriya

  • Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Abdul'aziz Yari, ya kai ziyara ga shugabannin addinin Musulunci a Jos, Kaduna da Bauchi
  • Yari ya gana da Sheikh Sani Yahaya Jingir, Khalifa Sheikh Ibrahim ɗan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi, da kuma shugabannin ƙungiyar JIBWIS
  • A lokacin ziyarar, Yari ya gargadi mutanen Arewa kan nacewa cewa dole ne shugabancin ƙasa ya ci gaba da zama a yankin sakamakon cewa hakan na iya raba kan ƙasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Abdul'aziz Yari, ya ƙara faɗaɗa tattaunawa da muhimman masu ruwa da tsaki.

Ya yi haka ne ta hanyar kai ziyara ga manyan shugabannin Darika da ƙungiyoyin Izala a birnin Jos, Kaduna da kuma jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Wakilan Tinubu sun je gidan Dahiru Bauchi, sun gargadi 'yan Arewa kan 2027

Sanata Abdulaziz Yari
Sanata Abdulaziz Yari da tawagar shi. Hoto: Abdulaziz Yari
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a X, Yari ya bayyana cewa ya ci gaba da zantawa da Sheikh Sani Yahaya Jingir a Jos da kuma Khalifa Sheikh Ibrahim, ɗa ga marigayi Sheikh Dahiru Bauchi a jihar Bauchi.

Tattaunawar tasu ta maida hankali ne kan hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa, yayin da suke ci gaba da samun goyon bayan jama'a domin manufar "Renewed Hope" ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Yari ya gargadi 'yan Arewa

A wani ɓangare na ziyarar, Yari ya kuma gana da shugabannin ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) a jihar Kaduna karkashin Sheikh Abdullahi Bala Lau.

Punch ta ruwaito cewa yayin da yake ziyara a Bauchi a gidan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi, Yari ya gargaɗi mutanen Arewa cewa kada su riƙa nacewa dole sai shugabancin ƙasa ya zauna a hannunta kowane lokaci.

Kara karanta wannan

Kabir Masari: Yadda wani dan Arewa ya zama dan gaban goshin Tinubu

Ya bayyana cewa:

"Idan muka ce babu wanda zai mulki Najeriya sai mutumin da ya fito daga Arewa, mun raba kanmu ke nan. Yana da matakar muhimmanci idan muna tare a matsayin ƙasa ɗaya haɗaɗɗiya, shugabanni su riƙa fitowa daga sassa daban-daban na ƙasar."
"A Najeriya, mun fara gano hanyar kiyaye haɗin kanmu da daidaito, wato shugabanci na fitowa daga sassa daban-daban na ƙasar. Idan aka zaɓi Shugaban Ƙasa daga Arewa, zaɓe na gaba ya kamata a zaɓi Shugaban Ƙasa daga Kudu. Shi ne mafita ga bambancinmu."
Sanata Abdulaziz Yari
Sanata Abdulaziz Yari a masallacin Sheikh Dahiru Bauchi. Hoto: MA TV
Source: Facebook

Yari ya buƙaci 'yan Najeriya da su goyi bayan tsarin shugabanci mai haɓaka haɗin kan ƙasa wanda ke bai wa sassa daban-daban damar fitar da Shugaban Ƙasa.

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa shugaban Darikar Qadiriyya, Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara ya nuna goyon bayan ga Bola Tinubu a 2027.

'Gwamnoni 5 za su tallafi NDC'

A wani labarin, mun ruwaito cewa shahararren ɗan kasuwa, Isaac Fayose, ya yi iƙirarin cewa gwamnonin jam’iyyar APC guda biyar suna goyon bayan jam’iyyar NDC a asirce gabannin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan mutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Fayose ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta wanda ya yaɗu sosai kuma aka yi ce-ce-ku-ce a kansa.

A cewar Fayose, gwamnonin guda biyar sun yi alƙawarin samar da tallafin kuɗi domin ɗaukar nauyin yaƙin neman zaɓen NDC, ko da yake ba za su fito fili ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng