‘Malaman Tsibbunka ne Suka Jawo Maka’: Fadar Shugaban Kasa Ta Dura kan Atiku
- Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da bala'in son mulkin Najeriya
- Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa Temitope Ajayi ya ce ikirarin Atiku game da shekarun Tinubu abin dariya ne
- Atiku ya ce yana da ƙoshin lafiya kuma zai iya jagorantar Najeriya, yayin da ya yi alkawarin shawo kan matsalar rashin tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar a matsayin mutumin da ke neman mulki ido a rufe.
Hakan ya biyo bayan kalaman Atiku inda ya ce Shugaba Bola Tinubu yana da shekaru 90 kuma ba shi da lafiya.

Source: Twitter
Temitope Ajayi, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a, ya bayyana kalaman Atiku a matsayin abin dariya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Atiku ya gano shaidar da ke nuna asalin shekarun Bola Tinubu a duniya
Fadar shugaban kasa ta dura kan Atiku
Ajayi ya ce Atiku Abubakar ba zai daina komai ba wajen ganin ya cimma burinsa na zama shugaban Najeriya, yana zargin tsohon mataimakin shugaban ƙasar da gaggawar neman cikar abin da malaman tsubbunsa suka yi masa annabci.
Ajayi ya ce:
“Ga Atiku Abubakar, wannan shi ne alamar ƙarshe na dokin da ke shirin mutuwa, ba zai tsaya ga komai ba saboda tsananin burinsa na shugabancin Najeriya.
“Yana fafutukar ganin ya cika abin da malaman tsibbunsa suka yi masa alkwari, mun ga irin abin da matsananciyar neman mulki za ta iya haifar wa mutum wanda ya kamata ya zama abin koyi wajen ladabi da kyakkyawar ɗabi'a a siyasa.
“Tsammanin kyakkyawar ɗabi'a daga mutumin da ke ƙarƙashin tsafin malaman tsibbu zai zama neman abin da ya wuce kima, wannan yawan mayar da hankali kan rayuwar Shugaba Bola Tinubu ta sirri ya zama abin da ya kamata a duba ta fuskar lafiyar kwakwalwa."

Source: Twitter
Abin da ke rikitar da APC game da Atiku
Hadimin Tinubu ya ce sun kasa fahimtar dalilin da ya sa mutumin da ya ce zai gudanar da kamfen ɗinsa ne kan batutuwan da suka shafi rayuwar ’yan Najeriya ya mayar da damar cimma burinsa zuwa magana kan rayuwar Shugaba Tinubu.
Ya ce abin dariya ne a ce Shugaba Tinubu yana da shekaru 90. Alhaji Atiku yana tashi kowace rana yana faɗin duk abin da ya zo bakinsa, da fatan kamfen ɗinsa da ke gazawa zai samu karɓuwa, cewar Punch.
Ya kara da cewa:
“Wannan shi ne dalilin da ya sa yake rikicewa tare da sauya matsayinsa kan batutuwan manufofi, yana kuma bayar da bayanai daban-daban a kowace rana.
“Lokacin da ya kasa gamsar da ’yan Najeriya kan inganci da yadda sabuwar manufarsa ta tallafin man fetur za ta yi aiki, hanyar da yake ganin zai ci gaba da kasancewa cikin labarai da kuma rayar da kamfen ɗinsa da ke durƙushewa ita ce ƙara kai hare-haren da suka shafi Shugaban Ƙasa."
Dan takarar gwamnan ADC ya gargadi Atiku
An ji cewa dan takarar gwamnan Adamawa na ADC, Alhaji Suleiman Omar, ya shawarci Atiku Abubakar kan tsoma baki cikin harkokin jam’iyyar.
Omar ya ce har yanzu shi ne halastaccen ɗan takarar gwamna na ADC a Adamawa, ya ce an yi zaɓen fitar da gwani ƙarƙashin kulawar INEC.
Ya ce ya shigar da ƙara a kotu kan sauya sunansa, kuma zai jira hukuncin kotu kafin yanke shawarar matakin da zai ɗauka na gaba.
Asali: Legit.ng

