Babbar Magana: Mutanen Garuruwa 2 a Najeriya Sun Yi Barazanar Mamaye Fadar Shugaban Kasa

Babbar Magana: Mutanen Garuruwa 2 a Najeriya Sun Yi Barazanar Mamaye Fadar Shugaban Kasa

  • Iyaye da mazauna Mussa da Lassa sun yi barazanar zuwa Fadar Shugaban Ƙasa cikin kwanaki shida idan ba a ceto ‘ya’yansu da aka sace ba
  • Yaran sun shafe sama da kwanaki 130 a hannun ‘yan ta’adda tun bayan sace su daga makarantunsu a watan Mayun 2026
  • Mazauna wadannan yankuna a jihar Borno sun buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaggauta ceto yaransu daga hannun yan ta'adda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Iyaye da mazauna yankuna Mussa da Lassa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba ta Jihar Borno sun yi barazanar yin tattaki zuwa Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Mutanen wadannan garuru sun yi barazanar mamaye fadar shugaban kasa daga nan zuwa kwanaki shida idan ba a ceto ‘ya’yansu da yan ta'adda suka sace ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Aso Rock.
Harabar fadar shugaban kasa da ke birnin tarayya Abuja Hoto: Aso Rock Villa
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa mazauna garuruwan na cikin damuwane sakamakon ‘ya’yansu da aka yi garkuwa da su, wadanda a yanzu suka shafe sama da kwanaki 130 a hannun ‘yan ta’adda.

Sun bayyana takaicinsu yayin wata zanga-zanga da suka gudanar kan abin da suka kira a matsayin rashin ɗaukar matakin da ya dace daga gwamnati a Askira/Uba

Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan Boko Haram/ISWAP sun sace yaran ne a lokacin wani jerin hare-haren garkuwa da mutane da ya faru a ranar 15 ga Mayu, 2026

A cewar iyayen, 'ya'yansu da aka yi garkuwa da su sun haɗa da yara 44 daga unguwar Mussa da kuma 36 wadanda dalibai ne daga makarantun Lassa.

Iyaye sun nemi Tinubu ya ceto yaransu

Shugaban tawagar iyayen, Ishaku Suya, wanda ya jagoranci kiran neman agajin, ya yi kira kai tsaye da kuma cikin nuna damuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu

“Muna wannan kira ga Shugaban Ƙasa cewa mu, iyayen yaran da aka sace na Mussa da Lassa, za mu mamaye titunan da ke kusa da Fadar Shugaban Ƙasa idan bai ceto yaranmu kamar yadda ya ceto yaran Oyo ba.

Kara karanta wannan

Maza 'yan daba sun shiga kwartanci dakunan dalibai mata a Taraba

"Ya kamata ko dai ya kashe mu, ya bar mu da rai, ko kuma ya ceto yaranmu,” in ji shi.
Borno.
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Dan Majalisa ya yi Allah-wadai

Dr Midala Usman Balami, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Askira/Uba da Hawul, shi ma ya yi Allah-wadai da tsawaita shiru da rashin ceto daliban.

“Makon da ya gabata, na shirya taron manema labarai da nufin jawo hankalin jama’a kan wannan batu, kuma muna magana da murya ɗaya: a ceto yaranmu,” in ji Balami

Ya bayyana cewa tuni ya gabatar da ƙuduri a Majalisar Ƙasa kan wannan mummunan lamari, tare da yin alƙawarin bibiyar batun.

Sojoji sun kashe yan ta'adda 1,1906 a Borno

Kun ji cewa Dakarun Operation Hadin Kai sun hallaka ’yan Boko Haram da ISWAP 1,106 tare da cafke sama da N300m na kuɗaɗen masu daukar nauyin ta'addanci.

Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai mai barin gado, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin jawabinsa na bankwana a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262