'Gwamnonin APC 5 za Su Juyawa Tinubu Baya a Zaben 2027,' Fayose

'Gwamnonin APC 5 za Su Juyawa Tinubu Baya a Zaben 2027,' Fayose

  • Shahararren ɗan kasuwa Isaac Fayose ya yi iƙirarin cewa gwamnonin jam’iyyar APC guda biyar suna goyon bayan jam’iyyar NDC a ɓoye
  • Fayose ya bayyana cewa gwamnonin sun alƙawarta za su ɗauki nauyin hidimar zaɓen jam'iyyar ta NDC a shirin zaɓen shekarar 2027
  • Ya ƙara da cewa gwamnonin ba za su fito fili su yi yaƙin neman zaɓe ko yin magana da za ta goya wa jam'iyyar baya ba domin su mambobin APC ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Shahararren ɗan kasuwa, Isaac Fayose, ya yi iƙirarin cewa gwamnoni biyar da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar APC suna goyon bayan jam'iyyar NDC a asirce gabannin zaɓen shekarar 2027.

Fayose ya bayyana cewa gwamnonin ba za su fito fili su yi yaƙin neman zaɓe ko fitar da wata sanarwa da za ta fito da su a matsayin masu goyon bayan NDC ba sakamakon matsayinsu na mambobin jam'iyyar mai mulki ta APC.

Kara karanta wannan

Tirkashi: ADC ta bankado makarkashiyar da ake kullawa a Arewa gabanin zaben 2027

Isaac Fayose Peter Obi na NDC
Isaac Fayose a hagu da Peter Obi a dama. Hoto: isaacfayoseoriginal/peterobi
Source: Instagram

Fayose ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya zarge su da alƙawarin samar da tallafin kuɗi domin ɗaukar nauyin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar NDC.

Me gwamnonin APC za su yi?

Fayose ya yi ikirarin cewa gwamnonin sun riga sun tattauna da su kan tsarin da za a bi wajen gudanar da zaɓen 2027.

Daily Post ta wallafa cewa ya ce:

"Yanzu muna da gwamnonin APC guda biyar da ke goyon bayan NDC a wannan zaɓen. Ba za su fito fili su yi mana yaƙin neman zaɓe ba. Ba za su faɗi komai a fili da zai kasance mai amfani gare mu ba, amma a ƙarƙashin ƙasa, sun yi mana alƙawarin ɗaukar nauyin wannan zaɓen, kuma buƙatarsu tana da sauƙi matuƙa."

Karin bayanin daga Fayose

Iƙirarin ya zo ne yayin da aka fara samun musayar kalamai tsakanin jam'iyyun hamayya da gwamnatin APC mai ci a lokacin da ake fuskantar zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Babban Sarki a Najeriya ya fito ya nuna goyon baya ga Tinubu

Fayose ya ci gaba da bayanin cewa babban abin da gwamnonin ba sa so shi ne Wike ya samu nasara a birnin tarayya Abuja da kuma jihar Rivers.

"Buƙatar tasu ita ce, ba sa son Wike ya ci FCT a ƙarƙashin APC; ba sa son Wike ya ci jihar Rivers a ƙarƙashin APC, na faɗa musu a taron cewa, Wike ba shi da karɓuwa a nan Abuja; APC ma ba ta da karɓuwa a nan Abuja.
"APC ba ta da karɓuwa a Rivers; tsarinsu shi ne su sace akwatin zaɓenmu, tsarinsu shi ne su bayyana sakamakon zaɓe, kuma sun ce eh, sun sani kuma abin da suke so shi ne kada su sami damar rubuta waɗancan sakamakon.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu a ofis. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yari ya gargadi 'yan Arewa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Abdul'aziz Yari, ya gargadi ga masu cewa mulki sai ya dawo Arewa.

Yari ya yi wannan gargaɗin ne a ranar Lahadi lokacin da yake jawabi ga taron shahararrun malamai a gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ke jihar Bauchi.

Ziyarar tana cikin tsarin tattaunawa da kwamitin ke yi da muhimman masu ruwa da tsaki gabannin gudanar da harkokin siyasa na gaba, yayin da kwamitin yake kewayawa jihohi daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng