'Zaɓen Atiku Kamar Jihadi ne': An Bayyana yadda Za a Kayar da Tinubu a 2027

'Zaɓen Atiku Kamar Jihadi ne': An Bayyana yadda Za a Kayar da Tinubu a 2027

  • An bayyana zaɓen Alhaji Atiku Abubakar a matsayin jihadi ga ƴan Najeriya, musamman saboda halin ƙunci da ake fuskanta a ƙasar
  • Wani hadimin dan takarar gwamnan Accord a Kano, Mukhtar Gashash ya ce Atiku zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu
  • Ya kuma yaba da ƙoƙarin Alhaji Musa Ibrahim Na-banki wajen kafa Ƙungiyar Ƴan Dan-Gwalen Atiku, domin tallafa wa takarar Atiku daga rumfunan zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wani hadimin dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar Accord, Mukhtar Gashash ya yabawa tsarin Atiku Abubakar.

Kwamred Murtala Mohammed ya ce zaben Atiku Abubakar a 2027 kamar jihadi ne saboda halin da ake ciki.

An bayyana yadda Atiku zai kayar da Tinubu
Dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar da Kwamred Murtala Mohammed. Hoto: Atiku Abubakar, Murtala Mohammed.
Source: Facebook

Murtala ya bayyana haka ne yayin zantawa da wakilin Legit Hausa a yau Asabar 29 ga watan Agustan 2027.

Ya ce suna gode wa Allah bisa ni’imar da Ya yi masu ciki har da ba su mutane irin Alhaji Atiku Abubakar, musamman a wannan mawuyacin hali da Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

'Malaman tsibbunka ne suka jawo maka': Fadar shugaban kasa ta dura kan Atiku

Murtala ya ce a duk lokacin da al’umma ta shiga ƙunci da matsaloli, Allah kan samar da mafita.

"A ganina, Atiku shi ne ɗan takara ɗaya tilo da zai iya kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, da ikon Allah.
"Kamar yadda na bayyana, zaɓen Atiku a wannan lokaci tamkar jihadi ne, saboda irin halin da muka tsinci kanmu a Najeriya.
"A gaskiya, sauran ƴan takarar da ake gani ba za su iya fafatawa da shi ba, idan ana magana ne bisa gaskiya ba tare da wasa ba."

Ya bayyana wata magana da Wazirin Adamawa ya yi, wacce ta sa Shugaba Tinubu da makarrabansa suka damu, ita ce batun dawo da tallafin man fetur.

Murtala ya ce ina daga ranar da Atiku ya yi wannan magana har zuwa yanzu, gwamnati na ci gaba da magana a kanta, duk da cewa akwai wasu muhimman abubuwan da ya yi alkawarin gyarawa.

"Daga cikin abubuwan da Atiku ya yi alkawarin farfaɗowa akwai tallafin da zai inganta rayuwar al’umma da tattalin arzikin ƙasa.

Kara karanta wannan

Rikicin ADC: An gargadi Atiku kan tsoma baki sha'anin jam'iyyar a Adamawa

"Hakan ya haɗa da samar wa matasa ayyukan yi da hanyoyin dogaro da kai, domin rage rashin aikin yi da ƙarfafa tattalin arzikin matasa.
" Ya kuma yi alkawarin dawo da tsaron rayukan ƴan Najeriya da dukiyoyinsu, domin jama’a su samu damar gudanar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali."

- Kwamred Murtala Mohammed

Ya ce wannan ne ya sa mutane irin Alhaji Musa Ibrahim Na-banki suke ci gaba da faɗakar da al’umma kada su yi wasa da muhimmancin takarar Atiku.

A cewarsa, Alhaji Na-banki na kira ga ƴan Najeriya da su zaɓi Atiku domin ceto ƙasar daga halin ƙuncin da take ciki.

Ya ce Na-banki yana matuƙar ƙoƙarin ganin Atiku ya samu nasara, ciki har da kafa ƙungiyar da ta fara daga rumfunan zaɓe zuwa mazabu da jahohi.

Adamawa: An gargadi Atiku kan shiga lamarin ADC

A wani labarin, an ji cewa dan takarar gwamnan Adamawa na ADC, Alhaji Suleiman Omar, ya shawarci Atiku Abubakar kan tsoma baki cikin harkokin jam’iyyar.

Omar ya ce har yanzu shi ne halastaccen ɗan takarar gwamna na ADC a Adamawa, ya ce an yi zaɓen fitar da gwani ƙarƙashin kulawar INEC.

Ya ce ya shigar da ƙara a kotu kan sauya sunansa, kuma zai jira hukuncin kotu kafin yanke shawarar matakin da zai ɗauka na gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.