Bayan Zurfafa Bincike, an Bankado Jami'an NSCDC 3 kan Mutuwar Mutum 37 a Neja
- Hukumar NSCDC ta dakatar da wasu jami’anta uku tare da bayar da umarnin saukar da tutocin ta na tsawon kwana uku
- Matakin ya biyo bayan mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne a hannun hukumar a Jihar Neja
- Rundunar ta ce za a gabatar da jami’an da aka dakatar ga kwamitocin bincike domin gudanar da cikakken bincike kan abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger – Rundunar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC) ta dakatar da wasu jami’anta uku kan mutuwar mutum 37 a Neja.
Ta kuma bayar da umarnin saukar da tutoci na tsawon kwana uku domin nuna alhini kan mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne.

Kara karanta wannan
Atiku ya jero mutane 3 da ya kamata su amsa tambayoyi kan mutuwar matasa 37 a hannun NSCDC

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa mai magana da yawun rundunar, Babawale Afolabi, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a Abuja.
Matakin da aka dauka a farko
Vanguard ta ruwaito cewa tun farko an dakatar da jami’an NSCDC 21 tare da kiran su zuwa hedikwatar rundunar da ke Abuja.
Matakin ya biyo bayan mutuwar akalla mutane 30 da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ne, waɗanda suka mutu a hannun rundunar a Jihar Neja.
Afolabi ya ce Kwamandan Janar na NSCDC, Ahmed Audi, ne ya bayar da umarnin saukar da tutocin domin nuna nadama, alhini da rashin amincewar rundunar kan lamarin.
Matakan da za a dauka
Audi ya ce matakin na nufin nuna cewa rundunar tana jimamin abin da ya faru tare da nuna ƙudirin kawar da jami’an da ba sa bin ƙa’idojin aiki.
Ya ƙara da cewa za a gabatar da dukkan jami’an da aka kama ko aka dakatar ga Kwamitin Bincike Mai Zaman Kansa da Shugaban Ƙasa ya kafa da sauran kwamitocin bincike.
Ya ce hakan zai ba da damar gudanar da ƙarin bincike tare da yiwuwar gurfanar da waɗanda aka samu da laifi.

Source: Original
NSCDC ta yi alƙawarin bayyana sakamakon bincike
NAN ta kuma ruwaito cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa na mutum 10 domin binciken abubuwan da suka shafi mutuwar waɗanda abin ya shafa.
Audi ya ce an kafa NSCDC ne bisa ƙa’idojin gaskiya, ƙwarewa, da’a da kuma cikakken mutunta dokokin ƙasa.
Ya ce rundunar ba za ta amince da rashin ƙwarewa wajen aiki, wuce gona da iri ko duk wani mataki da zai tauye haƙƙin ’yan ƙasa ba.
“Ba ma amincewa da rashin ƙwarewa wajen aiki, wuce gona da iri ko duk wani mataki da zai tauye haƙƙin ’yan ƙasa ko ya ci amanar amana mai tsarki da aka ba mu,”
In ji shi.
Ya kuma yi alƙawarin cewa NSCDC za ta ci gaba da sanar da jama’a sakamakon binciken da ake gudanarwa.
An hana fita a Neja
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, ya ayyana dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 a Minna, babban birnin jihar, bayan barkewar tarzoma a wasu sassan birnin.
An buƙaci mazauna Minna su zauna a gidajensu tare da kauce wa zirga-zirgar da ba ta zama dole ba a lokacin dokar hana fita.
Haka kuma, an buƙaci jami’an tsaro su tabbatar da aiwatar da dokar tare da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin birnin jihar.
Asali: Legit.ng

