Gwamnatin Tinubu Ta Yi Maganar Kara Kudin Wutar Lantarki a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Yi Maganar Kara Kudin Wutar Lantarki a Najeriya

  • Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya warware zare da abawa kan batun ƙara farashin wutar lantarki a yanzu
  • Gwamnati ta ce ta tara kimanin N1.23tn domin rage wani ɓangare na bashin N3.3tn da ke kan bangaren wutar lantarki
  • A cikin kwanaki 100 na farko na Tegbe, an sanya sababbin mitocin wutar lantarki kusan 350,000, inda adadin mitocin da aka sanya ya kai 1,004,260 zuwa Agusta 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta ce ba ta da wani shiri na ƙara farashin wutar lantarki a Najeriya.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan ranar Litinin, 21 ga watan Satumban 2026 yayin wata ganawa da manema labarai da aka gudanar a Abuja.

Gwamnatin tarayya ta ce ba zata kara kudin wuta
Ministan wutar lantarki, Joseph Tegbe na jawabi a wajen taro Hoto: Joseph Olasunkanmi Tegbe
Source: Twitter

An yi ganawa da manema labaran ne domin cika kwanaki 100 da ministan ya fara aiki, daga 8 ga Yuni zuwa 16 ga Satumban 2026, jaridar The Punch ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Ta tabbata Tinubu ba zai je Amurka ba, ya ba Shettima umarni kan taron UNGA

“Ba mu da shirin ƙara kudin wutar lantarki"

Tegbe ya ce gwamnati ta fi mayar da hankali kan inganta samar da wutar lantarki da kuma ƙarfafa harkar kuɗi da kayan aiki na bangaren wutar lantarki, maimakon ƙara wa masu amfani da wuta wasu kuɗaɗe.

“Bari na bayyana karara, kuma wannan ba maganar siyasa ba ce, ba mu da shirin ƙara farashin wutar lantarki.” In ji shi.

Gwamnati na son inganta bangaren wutar lantarki

Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na mai da hankali wajen magance matsalolin da ke hana bangaren wutar lantarki samun ci gaba.

Ya ce matsalolin sun shafi dukkan sassan tsarin samar da wuta, kuma akwai alaƙa tsakanin matsalolin, don haka ƙara samar da wuta kaɗai ba zai warware matsalar ba.

Kara karanta wannan

An farmaki magoya bayan Kwankwaso da Peter Obi a wurin gangamin siyasa, bidiyo ya fito

Tegbe ya ce lokacin da Tinubu ya ba shi amanar jagorantar ma’aikatar, ya yi wa ’yan Najeriya alkawura guda huɗu, TheCable ta dauko rahoton.

Ya ce ya yi alkawarin bin tsari mai inganci wajen magance matsalolin bangaren, tabbatar da daidaiton tsari ta hanyar gyare-gyare masu ma’ana da kuma samar da sauye-sauyen da jama’a za su iya gani a hankali.

Matsalar iskar gas na shafar samar da wuta

Ministan ya ce binciken da aka gudanar bayan ya kama aiki ya nuna cewa akwai matsaloli a kusan kowane mataki na tsarin samar da wutar lantarki.

Ya ce ƙarancin iskar gas da ake amfani da shi wajen samar da wuta na da alaƙa da lalacewar bututun iskar gas da kuma wasu sharuddan kasuwanci da ke rage sha’awar masu zuba jari.

Gwamnati ta tara N1.23tn kan bashin wuta

A bangaren kuɗi, Tegbe ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta tara kimanin N1.23tn domin magance wani ɓangare na bashin da ya tara a bangaren wutar lantarki.

Ya ce jimillar bashin da ke kan bangaren ya kai kusan N3.3tn.

Kara karanta wannan

APC ta yi zarge zarge masu nauyi kan Atiku, ta bukaci ya janye daga takara

Gwamnatin tarayya ta ce babu batun karin kudin wuta
Ministan wutar lantarki Joseph Tegbe Hoto: Joseph Olasunkanmi Tegbe
Source: Facebook

An sanya mitoci 350,000 cikin kwanaki 100

Ministan ya kuma bayyana cewa an sanya kusan 350,000 na mitocin wutar lantarki cikin kwanaki 100 na farko da ya yi a ofis.

Hakan ya sa jimillar mitocin da aka sanya ta kai 1,004,260 zuwa watan Agusta 2026.

Ya ce warware shari’ar da ta shafi shirin AMMON na samar da mitoci ya buɗe hanyar sayen wasu sababbin mitoci masu amfani da fasahar zamani kusan miliyan 1.4.

Za a cire tallafin lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da shirin kawo ƙarshen biyan tallafin wutar lantarki a Najeriya daga 2027.

Ministan wutar lantarki, Joseph Tegbe, ya ce za a cire tallafin ne domin samar da tsarin da zai dawwama a ɓangaren wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng