Ma'aikatan Gwamnatin Najeriya Sun Ji Wuta, Sun Tura Wasika Mai Zafi ga Shugaba Tinubu

Ma'aikatan Gwamnatin Najeriya Sun Ji Wuta, Sun Tura Wasika Mai Zafi ga Shugaba Tinubu

  • Ma'aikatan gwamnatin Najeriya sun koka kan karuwar wahalhalu da tsadar rayuwa sakamakon tashin farashin man fetur zuwa akalla N1,400
  • Bisa haka ma'aikatan suka rubuta tare da aika wasikar kokensu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu domin daukar matakin gaggawa
  • Sun nemi gwamnatin tarayya ta samar da wani da tsari na tallafi da zai rage tsadar man fetur zuwa N500 tare da kara mafi karancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ma’aikatan gwamnati da ke ƙarƙashin ɓangaren ƙungiyar ƙwadago ta JNPSNC sun rubuta wasika zuwa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ma'aikatan sun buƙaci Shugaba Tinubu ya yi gaggawar kawo dauki domin magance tsananin matsin tattalin arzikin da ke addabar ma’aikata da waɗanda suke dogaro da su.

Bol Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

An nemi Tinubu ya yi karin albashi

Vanguard ta ruwaito cewa ma’aikatan sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta daidaita farashin man fetur (PMS) zuwa N500 kan kowace lita, tare da ƙara albashi da alawus-alawus a dukkan ma’aikatan gwamnati.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan mutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Sun kuma buƙaci a kafa kwamiti nan take domin fara tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa kafin watan Janairun 2027.

A cikin wasiƙar da suka aika wa Shugaban Ƙasa, ma’aikatan sun ce ƙarin farashin man fetur zuwa N1,430 kan kowace lita ko fiye a wasu wurare ya ƙara tsananta matsalar tsadar rayuwa.

Ma’aikatan sun bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin zuwa Laraba, 30 ga Satumba, 2026, ta ɗauki mataki kan buƙatunsu, suna gargadin cewa tsananin wahalar da ake ciki na haifar da ɗimbin tashin hankali tsakanin ma’aikata da ‘yan Najeriya.

Ma'aikata sun tabo batun cire tallafi

JNPSNC ta ce cire tallafin man fetur shekaru uku da suka gabata ya haifar da gagarumin ƙarin farashin mai, lamarin da ya janyo hauhawar farashin muhimman kayayyaki.

Kungiyar ta ce wannan yanayi ya sanya rayuwa ƙara yin wuya ga ma’aikata, tana mai cewa rabon tallafin abinci ba zai iya zama mafita mai ɗorewa ga matsalar tattalin arzikin ƙasar ba.

Kara karanta wannan

Rikicin Wike da gwamnonin APC ya isa kasar Faransa, Tinubu zai masu sulhu a can

Ta ce,:

"Ma’aikatan Najeriya sun fahimci cewa rabon tallafi kamar buhunan shinkafa, Indomie, man girki, garri da sauran kayan abinci, tamkar ƙara ɗaure ‘yan Najeriya da talauci ne.
"Irin wannan mataki na ɗan lokaci ne, ba mai ɗorewa ba ne, mafi yawan al’ummar Najeriya ba sa iya samun sa, sannan kuma ya fi karkata ga ‘yan siyasa na kusa da gwamnati.”
Fetur.
Yadda ake hada hadar man fetur a gidajen mai a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ma’aikatan sun ce matakin da ya fi ɗorewa shi ne rage farashin man fetur zuwa N500 kan kowace lita, suna cewa hakan zai haifar da tasiri mai yawa a sassan tattalin arzikin ƙasa

Ta ce gwamnati na iya amfani da wani suna daban wajen bayyana wannan matakin idan kalmar “tallafin man fetur” ba ta dace da ita ba.

NLC ta yi maganar karin albashi

Kun ji cewa ƙungiyar NLC ta ce za ta dawo teburin tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan sabon mafi ƙarancin albashi, da ake neman a kara daga N70,000.

Ƙungiyar ta dage cewa albashin N70,000 da ake biya a yanzu ba ya isa wajen biyan muhimman buƙatun ma’aikatan kasar nan saboda dalilai da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262