Babbar Magana: Tinubu Ya Shigar da Kara Kotun Amurka kan Zargin da ake Masa
- Shugaba Bola Tinubu ya shigar da ƙara a wata kotun Amurka domin hana hukumomin ƙasar fitar da wasu bayanai da suka shafi zarge-zargen safarar ƙwayoyi
- Bayanai da wani mai fafutukar ganin an bayyana gaskiya a Amurka, Aaron Greenspan, ya nema sun haɗa da cikakken fayil ɗin FBI kan zarge-zargen
- Rahotanni sun nuna cewa lauyoyin Bola Tinubu sun ce fitar da bayanan na iya keta haƙƙin sirrin shugaban ƙasar da ke mulkar Najeriya a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington, D.C. – Shugaba Bola Tinubu ya shigar da ƙara a wata kotun Amurka domin ƙalubalantar yunƙurin fitar da bayanan da suka shafi zarge-zargen da ake yi masa na safarar miyagun ƙwayoyi.
Tinubu na ƙalubalantar Ma’aikatar Shari’a ta Amurka, FBI da DEA kan sakin bayanan da wani mai fafutukar ganin an samu gaskiya, Aaron Greenspan, ya nema.

Source: Facebook
Greenspan ya shigar da ƙara
Channels TV ta wallafa cewa Greenspan ya shigar da ƙarar neman bayanan ne ƙarƙashin dokar FOIA ta Amurka, inda yake neman takardun da suka shafi binciken hukumomin Amurka kan Tinubu.
Abubuwan da ya nema sun haɗa da cikakken fayil ɗin FBI da ya shafi Tinubu, da kuma bayanan tambayoyin FBI da suka shafi shekarun 1992 da 1993.
Har ila yau, ƙarar ta shafi wani bayanan da ake dangantawa da shari’ar kwace kadarori da aka gudanar a Amurka a shekarar 1993, inda ake magana kan kusan dala 460,000 da aka danganta da Tinubu.
Bukatar Tinubu a kotu
A cikin takardar kotu mai shafuka 16 da lauyoyinsa, Christopher W. Carmichael, Victor P. Henderson da Oluwole O. Afolabi, Tinubu ya ce sakin bayanan na iya tauye haƙƙinsa na sirri.
Lauyoyin sun kafa hujjar cewa kasancewar wasu bayanai sun taba fitowa a cikin bayanan jama’a ba ya nufin an kawar da haƙƙin mutum na kare sauran bayanan da ke cikin fayil ɗin bincike.
A cewar takardar, mutum na iya ci gaba da samun haƙƙin sirri kan cikakken fayil ko takardar bincike, ko da kuwa an taba bayyana wasu bayanai daga cikin fayil ɗin a baya.

Source: Facebook
Lauyoyin sun kuma yi nuni da wasu hukunce-hukuncen kotunan Amurka, suna cewa kasancewar an taba danganta mutum da wani binciken laifi ba ya nufin za a iya bayyana dukkan bayanan da ke cikin fayil ɗin binciken.
Nairametrcis ta wallafa a Facebook cewa sun ce:
“Ko da kuwa an bayyana wasu bayanai a baya yayin shari’ar kwace kadarorin, wanda ake magana a kansa har yanzu yana da haƙƙin sirri kan yiwuwar bayyana fayilolin binciken da mai ƙara ke nema.”
Tinubu na samun goyon baya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi watsi da ikirarin cewa masu zaɓe a Arewacin Najeriya na juya wa Shugaba Bola Tinubu baya.
Uba Sani ya yi hasashen cewa Tinubu zai iya samun tsakanin kashi 70 zuwa 80 na kuri’un da za a kada a Jihar Kaduna a zaben 2027.
Gwamnan ya ce al’ummar Kaduna ba sa yin siyasa bisa son zuciya, yana mai cewa za su tantance gwamnatin Tinubu ne bisa yadda take gudanar da mulki da kuma tasirin ayyukanta.
Asali: Legit.ng

