Musulunci Ya Yi Rashi: Ladanin Masallacin Harami Ya Rasu

Musulunci Ya Yi Rashi: Ladanin Masallacin Harami Ya Rasu

  • Ladanin Masallacin Harami da ke Makkah, Sheikh Ibrahim Al-Madani, ya rasu a safiyar Litinin, 21 ga Satumba 2026
  • Sheikh Ibrahim ya fara kiran sallah yana da shekaru 15 a wani masallaci da ke Madina, kafin daga bisani Allah ya kai shi Masallacin Harami
  • An shirya gudanar da sallar jana’izarsa a Masallacin Harami, sannan a binne shi a makabartar Jannatul Mu’alla

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Makkah, Saudiyya - Wani labari mai ban tausayi ya fito daga birnin Makkah, inda aka sanar da rasuwar Sheikh Ibrahim bin Adel Hamzah Al-Madani, daya daga cikin ladanan Masallacin Harami.

Sheikh Ibrahim ya rasu a safiyar Litinin, 21 ga Satumba 2026, wanda ya yi daidai da 10 ga Rabi’ul-Akhir 1448H, yana da kimanin shekaru 48.

Ladanin Masallacin Harami ya rasu
Sheikh Ibrahim Al-Madani yana kiran sallah Hoto: Haramain
Source: Facebook

Shafin Haramain ya sanar da rasuwar marigayin a Facebook ranar Litinin, 21 ga watan Satumban 2026 da safe.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Tsohon gwamna a Najeriya, Alhaji Ibrahim Idris ya rasu

Ya fara kiran sallah yana da shekaru 15

An haifi Sheikh Ibrahim bin Adel Hamzah Al-Madani a Madina ranar 8 ga Zul-Hijja 1397H. Ya taso ne a gidan addini, inda ya yi karatun Al-Qur’ani da sauran ilimin addini.

Kakan mahaifiyarsa ya kasance mahaddacin Al-Qur’ani, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen tarbiyyar Sheikh Ibrahim da kuma bunkasa alakarsa da Al-Qur’ani da ibada.

Sheikh Ibrahim ya fara kiran sallah tun yana dan shekara 15 a wani masallaci da ke Madina.

Daga bisani ya zama ladani a Masallacin Al-Maddah, kafin Allah ya karrama shi da nadinsa a matsayin ladanin Masallacin Harami a watan Ramadan na shekarar 1439H, wato 2018.

Ya hada salon kiran sallar Madina da Makkah

Duk da kasancewarsa dan asalin Madina kuma ya taso da salon kiran sallah na Madina, Sheikh Ibrahim ya kuma koyi salon kiran sallar Makkah.

An ce ya koyi wannan salo ne ta hanyar alakarsa da marigayi Sheikh Abdul Latif Mulla, wanda ya taba kasancewa cikin ladanan Masallacin Harami.

Kara karanta wannan

Sanata Barau Jibrin ya tsige hadimi saboda adawa da tazarcen Gwamna Abba a Kano

Muryarsa mai dadi ta zama sananniya ga miliyoyin Musulmi ta hanyar kiran sallah da kabbara da yake yi a Harami.

An ce ya kasance mai yawan ibada

Rahotanni sun bayyana cewa abin da ya fi ban sha’awa game da Sheikh Ibrahim ba wai muryarsa kawai ba ce, har ma da irin ibadar da yake yi a boye. An ce ya kan ware lokacinsa wajen ibada, musamman a karshen dare.

Mutanen da suka san shi sun bayyana shi a matsayin mutum mai yawan ibada, mai tsananin sadaukarwa da kuma kokarin kusantar Allah.

Za a yi jana’izarsa a Masallacin Harami

An bayyana cewa za a yi sallar jana’izar Sheikh Ibrahim Al-Madani a Masallacin Harami, sannan a kai gawarsa makabartar Jannatul Mu’alla domin binne shi.

Rayuwarsa ta fara ne da kiran sallah a Madina yana dan shekara 15, sannan ta kare bayan shekaru yana kiran miliyoyin Musulmi zuwa ga sallah daga Dakin Allah.

Allah Ya karbi dukkan kiran sallar da ya yi, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya daukaka darajarsa zuwa Jannatul Firdausi, kuma Ya sanya dukkan muryoyin da ya kira zuwa ga sallah su zama shaida a gare shi a ranar Alkiyama. Amin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Kano, an yi awon gaba da baarake

Ladanin masallacin Harami ya rasu
Marigayi Sheikh Ibrahim Al-Madani Hoto: Haramain
Source: Facebook

Tsohon gwamnan Kogi ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu ya koma ga Mahaliccinsa.

Marigayi Alhaji Ibrahim Idris ya rasu ne ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2026, a kasar Birtaniya yana da shekaru 77.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng