Bodejo: DSS Ta Cafke Shugaban Fulani na Miyetti Allah a Najeriya

Bodejo: DSS Ta Cafke Shugaban Fulani na Miyetti Allah a Najeriya

  • Jami’an DSS sun sake kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo, jim kaɗan bayan EFCC ta sake shi bisa cika sharudan beli
  • Iyaln Bello Bodejo sun nuna mamaki da takaici kan sake kama shi, suna cewa matakin jami’an tsaron bai dace da tsarin doka ba
  • Wata kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belinsa na Naira biliyan 2 a shari’ar da ake yi masa kan zargin halatta kuɗin haram na dala miliyan 2.63

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Jami’an Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) sun sake kama shugaban ƙungiyar Miyetti Allah, Bello Bodejo, bayan Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta sake shi bisa cika sharudan belinsa.

Iyalan shugaban na Miyetti Allah sun bayyana rashin jin daɗinsu kan sake kama shi, suna cewa matakin ya saɓa wa tsarin doka, musamman bayan da aka kammala dukkan sharudan da kotu ta gindaya na belinsa.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rutsa yan ta'adda masu karɓar kudin fansa a jihar Kebbi

Bello Bodejo a wajen taro
Shugaban Miyetti Allah a Najeriya, Bello Bodejo. Hoto: Bello Bodejo
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa jami’an DSS sun yi awon gaba da Bodejo zuwa hedikwatarsu ranar Juma’a, lamarin da ya jawo cece-kuce daga iyalinsa.

Yadda aka sake kama Bodejo

Hajiya Hauwa Bodejo, matar shugaban ƙungiyar, ta ce jami’an tsaro sun yi wa ƙofar hedikwatar EFCC kawanya na tsawon sa’o’i ranar Juma’a, yayin da ake shirin sakin mijinta.

Ta ce EFCC ta sanar da lauyoyin Bodejo a daren Alhamis cewa su zo tare da jami’an kotu domin a sake shi.

A cewarta, jami’an kotun sun bayyana cewa ba su da dalilin komawa EFCC saboda tuni sun miƙa takardar da ke tabbatar da cika sharudan belinsa.

Hauwa ta ce lokacin da suka isa hedikwatar EFCC, an riga an fitar da mijinta daga wurin da ake tsare da shi, ana jiran zuwansu domin a sake shi.

Sai dai ta ce yayin da suke barin harabar EFCC, jami’an DSS da suka kasance a wajen ƙofar hukumar suka ruga zuwa wajen Bodejo, suka yi awon gaba da shi cikin motoci uku.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga fadar Sarki, sun kashe shi bayan korafi kan ta'adinsu a Niger

Ana neman a yi masa adalci

Hajiya Hauwa ta sake jaddada buƙatar a yi wa mijinta adalci a shari'ar da ake yi masa, tana kuma nuna damuwa kan yadda lafiyarsa ke ƙara tabarbarewa.

PM News ta rahoto ta ce likitan Bodejo ya sha fuskantar hana shi ganinsa tun bayan kama shi a baya, wanda yanzu ta ce tsarewar ta kusan kai wa watanni uku.

Taswirar FCT, Abuja
Taswirar FCT, Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Har zuwa lokacin kammala rahoton, jami’an DSS ba su yi bayani a hukumance kan dalilin da ya sa aka sake kama Bodejo ba.

ADC ta nemi kama shugaban Kuje

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar ADC ta nemi a gaggauta gurfanar da shugaban Karamar Hukumar Kuje, Danjuma Shekwolo, bisa kalaman da ya yi kan mazauna yankin.

Jam’iyyar ta ce Shekwolo ya yi barazanar korar mazauna Kuje da ba sa goyon bayan jam’iyyar APC, bayan ya bukaci su goyi bayan jam’iyyar ko su bar yankin.

ADC ta bayyana kalaman a matsayin “barazanar tilasta wa mutane yin hijira” da kuma kai hari ga haƙƙoƙin tsarin mulkin Najeriya na mazauna Kuje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng