Ana Wata ga Wata: Atiku Ya Gano Shaidar da ke Nuna Asalin Shekarun Bola Tinubu a Duniya

Ana Wata ga Wata: Atiku Ya Gano Shaidar da ke Nuna Asalin Shekarun Bola Tinubu a Duniya

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar ya ce yana da hujjar da ke nun asalin shekarun Bola Tinubu
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce yana da shaidar cewa Shugaba Bola Tinubu yana da shekara 90 a duniya
  • Atiku ya ce a shirye yake ya gabatar da hujja a gaban kotu idan aka kai shi kara, yana mai jaddada bukatar magance matsalar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben 2027, Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kai shekara 90 a duniya.

Atiku ya bayyana cewa yana da cikakkiyar hujjar da ke nuna Tinubu ya kai shekara 90, sabanin shekarun da yake amfani da su a yanzu watau 74.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: A ɗauko hoton shekaru 30 da suka gabata don kare yawan shekarun Tinubu

Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar yana sa hannu Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku Abubakar ya ce shekarun Tinubu 90

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC, yayin da yake bayanin dalilin da ya sa yake ganin ya cancanci sake neman shugabancin Najeriya.

“Yanzu muna da shugaban kasa mai shekara 90, kuma ba shi da lafiya. Ni ina cikin koshin lafiya, ina da karfi. To, me zai hana in ba ‘yan uwana ‘yan kasa gudunmawar da zan iya?” Atiku ya tambaya.

Ya kara da cewa yana da hujjar da za ta tabbatar da cewa Tinubu yana da shekara 90 a duniya, yana mai cewa zai gabatar da ita a gaban kotu.

Atiku ya bayyana dalilin takararsa

Da yake magana kan tarihin siyasarsa, Atiku ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba shi damar sake neman shugabancin kasar.

Dan takarar na ADC ya ce ya taba neman kujerar gwamna har sau hudu, amma hukumomin soji da ke jagorantar sauyin mulkin Najeriya zuwa dimokuradiyya sun hana shi tsayawa a wasu lokuta.

Kara karanta wannan

'Na san ainihin shekarun shugaba Tinubu': Atiku ya ce yana da hujjoji masu ƙarfi

“Na tsaya takarar gwamna har sau hudu, saboda a lokacin mutanen da ke jagorantar sauyin Najeriya zuwa dimokuradiyya sojoji ne, kuma ina matukar adawa da mulkin soja.
“Duk lokacin da na yi nasara, sai su hana ni. A karshe ma an yi yunkurin kashe ni, amma na tsere zuwa gudun hijira,” in ji shi.
Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock da ke Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Atiku ya ce ba kasafai yake samun abubuwa cikin sauki a rayuwarsa ba, yana mai cewa yawan takarar shugaban kasa da ya yi ba wani sabon abu ba ne a tarihin siyasarsa.

Ya ce yana da kwarewa, cancanta da kishin kasa, don haka yana ganin ya dace ya yi amfani da wadannan abubuwa wajen yi wa Najeriya hidima.

Atiku ya dage kan dawo da tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar ya ce bai yi adawa da cire tallafin man fetur ba, amma yana tambayar inda kudaden da aka samu daga cire shi suka tafi.

A cewarsa , kudaden da aka samu ya kamata a karkatar da su wajen inganta rayuwar jama’a, musamman ta hanyar rage talauci da tallafawa harkar ilimi.

Atiku ya ce rashin sanin ina kudin shiga shiga, ya sa yake tunanin zai dawo da tallafin man fetur idan aka zabe shi a 2027, domin rage radadin da tattalin arziki ya jefa ‘yan Najeriya ciki

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262