Rikicin ADC: An Gargadi Atiku kan Tsoma Baki Sha’anin Jam’iyyar a Adamawa
- Dan takarar gwamnan Adamawa na ADC, Alhaji Suleiman Omar, ya shawarci Atiku Abubakar kan tsoma baki cikin harkokin jam’iyyar
- Omar ya ce har yanzu shi ne halastaccen ɗan takarar gwamna na ADC a Adamawa, ya ce an yi zaɓen fitar da gwani ƙarƙashin kulawar INEC
- Ya ce ya shigar da ƙara a kotu kan sauya sunansa, kuma zai jira hukuncin kotu kafin yanke shawarar matakin da zai ɗauka na gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Yola, Adamawa - Dan takarar gwamna na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Adamawa ya gargadi Atiku Abubakar.
Alhaji Suleiman Omar, ya bukaci tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya nisanci harkokin jam’iyyar ADC.

Source: Twitter
Omar ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Yola ranar Juma’a, inda ya ce sauya sunansa da Atiku ya yi ba bisa kundin tsarin mulki ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Ana wata ga wata: Atiku ya gano shaidar da ke nuna asalin shekarun Bola Tinubu a duniya
Dan 'takarar' gwamnan ADC ya gargadi Atiku
Ya ce har yanzu shi ne halastaccen ɗan takarar gwamna na ADC a Adamawa, yana mai cewa ba za a iya maye gurbinsa ta hanyar da ba ta dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.
Omar ya ce yana kira ga Atiku da ya janye wannan matsaya tare da kaurace wa duk wani mataki da zai iya kawo cikas ga tsarin da jam’iyyar ta bi, wanda kuma yanzu yake gaban kotu.
Ya ce jagoranci yana bukatar kamun kai, adalci da mutunta bin doka, musamman daga mutanen da ke da burin jagorantar ƙasa, yana mai cewa ikon siyasa na hannun jama’ar da suka bayar da shi ne.

Source: Facebook
Dan takarar ADC ya fadi yaddaaka zabe shi
Omar ya bayyana cewa har yanzu shi ne wanda aka zaɓa bisa ƙa’ida a matsayin ɗan takarar gwamna na ADC a Adamawa, kuma ba za a iya maye gurbinsa ta hanyar da ba ta dace da dimokuraɗiyya ba.
Ya ce an gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamnan jam’iyyar ƙarƙashin kulawar Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), kuma ‘yan jam’iyya da jama’a sun halarta.
Omar ya ce shi ne ya yi nasara a zaɓen, yayin da Alhaji Tukur Modibbo ya zo na biyu, sannan aka miƙa sunansa ga INEC a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
Ya ƙara da cewa ya garzaya kotu domin neman umarnin hana INEC karɓar duk wani sauya sunansa da jam’iyyar ko wani mutum zai yi, cewar Tribune.
Omar ya ce an isar da takardun shari’ar ga INEC da jam’iyyar, a matakin ƙasa da na jiha, kuma an sanar da Atiku Abubakar game da matakin da ya ɗauka.
Ya ce har sai kotu ta yanke hukunci, babu wani mutum, ko da kuwa yana da matsayi ko tasiri, da ke da ikon sauya sakamakon zaɓen fidda gwani ko fifita ra’ayinsa kan zaɓin ‘yan jam’iyya.
Omar ya ce idan za a iya soke ƙuri’un ‘yan jam’iyya bayan an gudanar da zaɓe, hakan ba zai inganta dimokuraɗiyya ba, illa dai zai maye gurbinta da rashin hukunci da ‘yan Najeriya suka dade suna ƙi.
Ya yi kira ga dukkan ‘yan jam’iyyar ADC, magoya bayansa a Adamawa da sauran ‘yan Najeriya da su kasance cikin natsuwa, lura da al’amura da kuma jajircewa.
ADC ta musanta sauya dan takararta a Adamawa
Kun ji cewa jam'iyyar ADC a Adamawa ta yi martani kan rahotannin da suke yawo game da maye gurbin ɗan takararta, Ambasada Injiniya Omar Suleiman.
Jam'iyyar ta ce Omar Suleiman ne halastaccen ɗan takara, babu batun janye takara, maye gurbinsa ko wata tattaunawar sauya sunansa.
ADC ta ce shugabannin ƙananan hukumomi 21 sun tabbatar da goyon bayansu gare shi, tare da roƙon al'umma su yi watsi da jita-jita.
Asali: Legit.ng

