Matawalle Ya Dawo da Karfinsa, Ya Yi Alƙawarin Ƙuri'u Miliyan 20 ga Tinubu

Matawalle Ya Dawo da Karfinsa, Ya Yi Alƙawarin Ƙuri'u Miliyan 20 ga Tinubu

  • Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya kaddamar da kungiyar ‘Tinubu Again’, wadda ke shirin yi wa Bola Tinubu gata
  • Matawalle ya ce kungiyar za ta kai sakon manufofin gwamnatin Tinubu kai tsaye ga jama’a a matakin kasa da gida-gida
  • Ya bayyana cewa kungiyar za ta tallafa wa dukkan ’yan takarar APC, gwamnoni, sanatoci, ’yan majalisar wakilai da majalisun jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya kafa wata kungiyar tattara magoya baya mai suna ‘Tinubu Again’.

Matawalle ya yi alkawarin samar da kuri’u sama da miliyan 20 ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC a babban zaben 2027.

Matawalle ya yi wa Tinubu alkawarin miliyoyin kuri'u
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Original

Matawalle ya bayyana hakan ne bayan dawowarsa Najeriya, inda mambobin kungiyar suka tarbe shi, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Ko Tinubu na da abubuwan da zai shawo kan 'yan Najeriya su zaɓi APC a 2027? An samu bayani

Gudunmawar da Matawalle ya ba kamfen Tinubu

A wani bangare na shirye-shiryen yakin neman zaben, ministan ya kuma gabatar da motoci 50 da aka tanada domin gudanar da ayyukan kungiyar ‘Tinubu Again’.

Matawalle ya ce kungiyar za ta tattara magoya baya domin gudanar da yakin neman zabe gida-gida, don tallafa wa Tinubu da sauran ’yan takarar APC, ciki har da gwamnoni, sanatoci, ’yan Majalisar Wakilai da ’yan majalisun dokokin jihohi.

Ya ce manufar kungiyar ita ce kai sakon gwamnatin Tinubu kai tsaye ga ’yan Najeriya a matakin tushe, tare da bayyana manufofi da shirye-shiryen gwamnatin tarayya.

Ya ce Shugaban yana da kyakkyawar niyya ga ’yan Najeriya, amma ya jaddada cewa wajibi ne magoya bayansa su kai sakon gwamnatin zuwa ga jama’a.

Matawalle ya ce:

“Dole mu gangara cikin jama’a domin sanar da mutane, wayar da kan su kan abin da wannan gwamnati ke yi, abin da Bola Ahmed Tinubu yake yi wa jama’a, shirye-shiryensa, hangen nesansa, manufofinsa da abin da yake son yi wa ’yan Najeriya.

Kara karanta wannan

'Ya danganta da Tinubu': Atiku kan yiwuwar halartar muhawarar shugaban kasa

“Yana da kyakkyawar niyya, amma dole mai isar da sakon ya gangara cikin jama’a domin ya sanar da su cewa wannan shi ne abin da wannan mutum yake shirin yi kuma ya kuduri aniyar yi wa ’yan Najeriya.”
Matawalle zai tallata Tinubu gida-gida
Karamin ministan tsaro a Najeriya, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Twitter

Gudunmawar da kungiyar za ta bayar

A cewar Matawalle, kungiyar ba za ta tsaya kan zaben shugaban kasa kadai ba, domin za ta kuma tattara goyon baya ga ’yan takarar APC na sauran mukaman zabe.

Ministan ya ce kungiyar tana da burin tattara masu kada kuri’a sama da miliyan 20, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa hakan zai taimaka wajen samun nasarar Tinubu da ’yan takarar APC a 2027, cewar Daily Post.

Ya ce:

“Za mu yi aiki dare da rana domin tabbatar da nasarar su, mu tabbatar mun kai su ga nasara, da dukkan ’yan takararmu, ko gwamnoni, sanatoci, ’yan Majalisar Wakilai, ’yan Majalisar Jiha da sauran mukaman zabe.
“Wannan kungiya a shirye take ta tattara mutane sama da miliyan 20 domin tabbatar da nasarar dukkan ’yan takarar APC, na kasa da na jihohi.”

Ya ce yakin neman zaben na matakin tushe zai kunshi kai kungiyar zuwa al’ummomi da tattaunawa kai tsaye da masu kada kuri’a.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da matsala har a majalisa daga nadin kwamitin yakin neman zabe

Kamfe: An yaba wa Tinubu kan mutunta Matawalle

An ji cewa Ma’aikatar Tsaro ta yaba da naɗin Bello Matawalle a cikin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu na 2027.

Ma’aikatar ta ce naɗin ya nuna amincewar Tinubu da ƙwarewar Matawalle wajen gudanar da harkokin gwamnati.

Matawalle ya gode wa Tinubu da shugabannin APC, tare da yin alƙawarin amfani da ƙwarewarsa wurin tara masa kuri'u.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.