Abba Kabir Yusuf Ya Yaba wa Sheikh Jingir kan Muslim Muslim a 2027

Abba Kabir Yusuf Ya Yaba wa Sheikh Jingir kan Muslim Muslim a 2027

  • Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwarorinsa na Yobe, Sokoto da Jigawa sun yaba wa Sheikh Sani Yahaya Jingir kan kokarinsa na tabbatar da hadin kai
  • Kungiyar JIBWIS ta bukaci mambobinta a fadin Najeriya su goyi bayan shugaban kasa Bola Tinubu da Kashim Shettima a zaben 2027
  • An kuma bayyana cewa tallafin N300m da Gwamna Mai Mala Buni ya yi wa jami'a Izala kyauta ce ta kansa, ba ta gwamnatin jihar Yobe ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da takwarorinsa na jihohin Yobe, Sokoto da Jigawa, sun yaba wa shugaban majalisar malamai na Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir.

Gwamnonin sun jinjinawa Sheikh Jingir kan irin kokarinsa na tsawon lokaci wajen inganta hadin kai, zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin Musulmi da sauran 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Yobe ta yi magana kan ba Izala Naira miliyan 300

Abba Kabir Yusuf da Sheikh Sani Yahaya Jingir
Sheikh Sani Jingir a dama da Abba Kabir Yusuf a hagu. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa|Hamza Muhammad Sani
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook a ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2026.

JIBWIS ta goyi bayan Tinubu

An bayyana hakan ne a wani taron kasa na yini daya mai taken inganta shiga harkokin siyasa da goyon bayan tabbatar da adalci domin samar da hadin kai da ci gaba a Najeriya.

An gudanar da taron ne a Saddiqa Event Centre da ke birnin Jos, jihar Plateau, inda manyan malaman addini, 'yan siyasa da jami'an gwamnati suka halarta.

A yayin taron, kungiyar JIBWIS ta bukaci mambobinta a fadin Najeriya su goyi bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu da gwamnan Yobe sun ba Izalar Jingir Naira miliyan 600

Shugaban gudanarwa na kungiyar JIBWIS, Sheikh Abdulnasir Abdulmuhuyi, ya bayyana gamsuwarsa da gwamnatin Tinubu da Shettima.

Ya ce gwamnatin tarayya ta nuna jajircewa da rikon amana wajen gudanar da ayyukan raya kasa cikin shekaru ukun farko na mulkinta.

A cewarsa, gwamnatin ta cancanci a ba ta damar zarcewa domin ci gaba da ayyukan raya kasa da kuma karfafa nasarorin da ta samu.

Wajen da aka yi taron Izala
Manyan 'yan siyasa da Sheikh Sani Yahaya Jingir a taron Izala. Hoto: Barau I Jibrin
Source: Facebook

Bayanin gwamnan Yobe

Da yake magana a madadin gwamnoni Abba Kabir Yusuf na Kano, Ahmed Aliyu na Sokoto, Umar Namadi na Jigawa da Mai Mala Buni na Yobe, Gwamna Buni ya tuna da tarihin siyasar Najeriya.

Ya kawo misalin zaben shugaban kasa na 1993, lokacin da marigayi MKO Abiola ya tsaya takarar shugaban kasa tare da Ambasada Babagana Kingibe a matsayin mataimakinsa.

Gwamna Buni ya yaba wa Sheikh Jingir kan jajircewarsa wajen amfani da wa'azinsa domin karfafa hadin kan kasa da zaman lafiya tsakanin al'ummomin Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaban APC ya sauka a Kano, ya yi ganawar sirri da Sarki Sanusi II

Bayanin ba Izala N300m

A wani labarin, mun kawo cewa mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabir Masari, ya sanar da bayar da Naira miliyan 300 a matsayin gudummawarsa ga jami'ar Izala.

Masari ya ce gwamnan Yobe ma ta alkawarin bayar da wata Naira miliyan 300 a madadin Mai Mala Buni domin tallafa wa jami'ar da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya kafa.

Sai dai wata sanarwa daga bangaren gwamnatin jihar Yobe ta yi karin bayani kan batun bayan wasu muhawara da suka taso a kafafen sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng