Da Gaske Naja’atu Mohammed Ta Tura Tawaga domin ba Isa Pantami Hakuri?

Da Gaske Naja’atu Mohammed Ta Tura Tawaga domin ba Isa Pantami Hakuri?

  • Naja’atu Mohammed ta musanta rahoton cewa ta tura tawaga ta musamman domin neman afuwar Farfesa Isa Ali Pantami
  • Yar siyasar ta ce har yanzu tana kan matsayinta na cewa Pantami makaryaci ne, tana mai cewa ba ta tattauna da kowa kan batun
  • Naja’atu ta kuma bayyana cewa ba ta san wani na kusa da Pantami ba, kuma idan wasu sun je wurinsa, sun tafi ne da kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Pantami, Gombe - Yar siyasa a Najeriya, Naja'atu Mohammed ta yi martani kan wani rahoto da ake yadawa game da ita.

Naja'atu ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta tura tawaga ta musamman domin ba Farfesa Isa Ali Pantami hakuri.

Naja'atu ta musanta ba Pantami hakuri
Sheikh Isa Pantami yana gabatar da makala a taron Injiniyanci karo na 5 a jami'ar BUK, da Hajiya Naja'atu tana magana a shirin Ali Jita. Hoto: @ProfIsaPantami/X, Ali Jita Multimedia/YouTube.
Source: UGC

Yar siyasar ta bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da shafin ya yi hira da ita wanda aka wallafa a Facebook a yau Lahadi.

Kara karanta wannan

Atiku ya kalubalanci dalilin FBI ta 'boye' bayanai game da Tinubu

Sukar Pantami da Naja'atu ta yi a baya

Naja'atu ta yi karin haske ne game da jita-jitar da ake yadawa bayan wasu kalaman da ta yi a baya kan Pantami.

A wancan lokaci, ta kwatanta Pantami da makaryaci wanda ke pantama karya ba tare da jinkunyar komai ba.

Sai dai a martaninta, ta bayyana cewa babu wanda ta tura domin ba Pantami hakuri, kuma tana kan bakarta na cewa shi makaryaci ne.

Ta ce:

"Gaskiyarta shi ne Pantami ya dada fantama karya, makaryaci ne, mutanensa makaryata ne, ban fadi wannan ba, ban zauna da kowa a kan maganar Pantami ba.
"Ban san ma wani ko wasu mutanen Pantami ba, babu wanda ya taba mini magana a kan cewar za a tura mutane domin magana da Pantami.
"Saboda haka wandannan su ma masu fantamawa ne kamar yadda shi ma yake fantamawa, wannan ta tabbatar da Pantami da mutanensa makaryata ne."

Kara karanta wannan

Cibiyar BBYDI za ta horar da mata kan ilmin amfani da fasahar AI a Kaduna

Naja'atu ta sake caccakar Pantami
Yar siyasaa Najeriya, Naja'atu Mohammed tana jawabi a wurin taro. Hoto: Naja'atu Mohammed.
Source: Facebook

Naja'atu ta yi takaici kan halayen Pantami

Naja'atu ta bayyana cewa karyar ta zame wa yan Pantami jiki sai dai masu son shi su yi masa addu'a saboda siffofin munafuki sun shafe shi.

Ta tabbatar da cewa ba ta tura kowa ba kuma bata san wani na kusa da Pantami ba, idan ma wasu sun je to sun je a karan kansu bata sani ba.

"Karyar ta zame masu ciwo yadda ba za su iya rayuwa ba sai sun yi, babu siffofin munafukai da ba su nuna ba.
"Ban taba jin labarin wani mutum na jikin Pantami ba, idan ma sun je sun zauna da su ban san za su je ba, ban yi magana da su ba, idan ma sun yi haka to suma sun fantama karya."

- Naja'atu Mohammed

Naja'atu ta fadi yadda ADC za ta ceci Najeriya

A baya, an ji cewa fitacciyar ƴar siyasa a Najeriya, Hajiya Najaatu Muhammad ta ce ADC ce injin ceto Najeriya daga bakin da ta ke ciki a 2027.

Kara karanta wannan

Sojoji sun bi sawun yan bindiga da aka raunata, an kama mutum 2 da ke jinya a Adamawa

A yayin da ta ke jawabi a wajen babban taron jam'iyya da ya gudana a Abuja, ta ce zaɓe mai zuwa ba wai tsakanin ADC da APC ba ne.

Ta bukaci ‘yan Najeriya su hada kai domin kawo karshen mulkin rashin adalci da ta ce ana yi masu a ƙarƙashin mulkin Bola Tinubu da APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.