Yan Bindiga Sun Harbe Shugaban Jam'iyyar APC, Sun Tafi da Mutumin da Suke Tare

Yan Bindiga Sun Harbe Shugaban Jam'iyyar APC, Sun Tafi da Mutumin da Suke Tare

  • ‘Yan bindiga sun kashe shugaban jam'iyyar APC na Dekina, Ishaq Yunusa, a jihar Kogi da ke yankin Arewa ta Tsakiya a Najeriya
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun bude wa masu ababen hawa wuta a kan hanyar Itobe-Ochadamu, lamarin da ya yi ajalin Yunusa
  • ‘Yan sanda sun fara farautar wadanda suka sace wani fasinja tare da cafke maharan da suka aikata wannan danyen aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi, Nigeria - Miyagun ‘yan bindiga sun kashe shugaban jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Dekina ta Jihar Kogi, Hon. Ishaq Yunusa, tare da yin garkuwa da wani mutum da ke cikin motarsa.

Lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 27 ga watan Agustan 2026 a kan babbar hanyar Itobe-Ochadamu, kusa da Ojuwo Olijo da ke Karamar Hukumar Ofu ta jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun shammaci ƴan bindiga suna shirin satar kaya a tirela, sun kashe 17

Kogi.
Taswirar jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta ruwaito vewa Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kogi, ASP Afusat Saliu, ta tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a Lokoja ranar Juma’a.

Yan bindiga sun bude wuta

Afusat Saliu ta ce harin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yamma, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka fito daga dajin da ke kusa da hanyar suka bude wa masu ababen hawa wuta.

Ta ce daga bisani an gano wata motar Toyota Corolla mai launin shudi, mai lambar rajista GWA 636 CH, a tsaye a gefen babbar hanyar.

“An gano direban, wanda aka bayyana a matsayin Hon. Ishaq Yunusa, ya mutu a cikin motar, yayin da maharan suka tafi da wani mutum da ke cikin motar zuwa cikin daji,” in ji sanarwar.

Yan sanda sun dauki mataki

Kakakin ‘yan sandan ta ce rundunar, tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, ta kara tsaurara ayyukan sintiri da bincike a yankin, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Neja: Bayan umarnin Tinubu, an gano abin da yan sanda ke yi don ceto masallata da aka sace

Ta ce jami’an tsaro suna binciken dazuzzukan da ke kewaye da wurin domin gano tare da ceto wanda aka yi garkuwa da shi, da kuma cafke wadanda suka kai harin.

Ta ce an kai gawar Yunusa Asibitin Grimard da ke Anyigba domin gudanar da binciken gawar, yayin da jami’an tsaro ke bin dukkan wasu alamu da za su taimaka wajen gano wadanda suka aikata laifin.

Yan sanda.
Jami'an rundunar yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: PoliceNG
Source: Twitter

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kogi, CP Naziru Bello Kankarofi, ya bayar da umarnin ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a kan hanyar da lamarin ya faru.

Ya kuma umarci jami’an da su tabbatar an gano tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a kisan da sace mutumin.

Shugaban APC ya rasu a wurin taro

A wani labarin, kun ji cewa shugaban jam’iyyar APC mai mulki na karamar hukumar Ijumu ta jihar Kogi , Oyewole Mayowa Solomon, ya yi bankwana da duniya.

Marigayin ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya fadi a lokacin da ake gudanar da wani taron sasanta rikicin jam’iyyar a ranar Juma’a, 21 ga watan Agustan 2026.

An ba shi agajin gaggawa a wurin taron kafin a tafi da shi zuwa wani asibiti da ke Kabba, inda aka tabbatar da cewa ya rasu tun kafin a isa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262