Matakin da Gwamna Bago Ya Dauka kan Mutuwar Mutane 37 a Hannun NSCDC

Matakin da Gwamna Bago Ya Dauka kan Mutuwar Mutane 37 a Hannun NSCDC

  • Gwamnatin Neja ta soke gangamin APC da aka shirya gudanarwa a Minna bayan mutuwar mutane 37 da ke tsare a hannun NSCDC
  • Gwamna Umaru Bago ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki domin girmama waɗanda suka mutu tare da jajanta wa iyalansu
  • Gwamnatin jihar ta rufe wurin haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba da ke MiOshishi, inda ta ce ana gudanar da ayyukan ba tare da isassun kayan tsaro ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Gwamnatin Jihar Neja ta soke gangamin siyasar All Progressives Congress (APC) da aka shirya gudanarwa ranar Asabar a Minna, babban birnin jihar.

An ɗauki matakin ne bayan mutuwar mutane 37 da rahotanni suka ce suna tsare a hannun Hukumar NSCDC a jihar Neja.

Bago ya soke gangamin APC
Gwamna Bago na jawabi a wajen taro Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

Bago ya ayyana zaman makoki

Tashar Channels tv ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran gwamnan Neja, Bologi Ibrahim, ya fitar.

Kara karanta wannan

Ta tabbata mutane sun mutu a hannun NSCDC, Gwamna Bago ya fadi halin da ake ciki

Gwamna Umaru Bago ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu, sannan ya kuma ayyana kwanaki uku na zaman makoki domin girmama mamatan.

Gwamnatin jihar ta ce an soke gangamin ne saboda munanan abubuwan da suka faru, da kuma nuna girmamawa ga mamatan da iyalansu.

Gangamin APC da aka soke zai kasance wani ɓangare na ayyukan siyasar jam’iyyar a jihar, kuma an shirya gudanar da shi a Minna a wannan ƙarshen mako.

Gwamnati ta umarci hukumomi su dauki mataki

Gwamnatin Neja ta kuma umarci hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan da suka dace dangane da lamarin.

Bago ya kuma sanar da rufe wurin haƙar ma’adinai da ke yankin MiOshishi, yana mai cewa ana gudanar da ayyukan haƙar ma’adinan ba tare da amfani da fasahar da ta dace da kayan aikin kare lafiyar ma’aikata ba.

Bago ya yi kira ga matasa su guji rikici

Gwamnan ya yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan kai gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa ɗakin ajiye gawarwaki, lamarin da ya ce ya jawo tashin hankali da martanin wasu matasa.

Kara karanta wannan

An dakatar da babban jami'in tsaro kan mutuwar kusan mutum 40

“Muna kira ga dukkan matasanmu da su guji tashin hankali. Ba zai dawo da waɗanda suka mutu ba. A ƙarshe zai jawo mana babbar asara,” in ji Bago.

Ya buƙaci matasan jihar su guji ɗaukar doka a hannunsu, yana mai cewa tashin hankali ba zai magance matsalar da ta faru ba.

Ana shirya sunayen mamatan

Bago ya ce gwamnatin jihar tana tattara jerin sunayen waɗanda suka mutu domin samun damar gano iyalansu da kuma tuntuɓar su.

Ya sake mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan, tare da addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu, Ya kuma ba iyalansu da sauran ’yan uwansu haƙurin jure wannan babban rashi.

Mutane sun mutu a Niger
Taswirar jihar Neja, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An dakatar da kwamandan NSCDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakatar da kwamandan rundunar NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, sakamakon mutuwar wasu da ake zargin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayar da umarnin dakatar da kwamandan nan take tare da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng