Ana Batun Abin da Ya Faru a Ofishin NSCDC, Matasa da Dama Sun Sake Mutuwa a Arewa

Ana Batun Abin da Ya Faru a Ofishin NSCDC, Matasa da Dama Sun Sake Mutuwa a Arewa

  • Mutane da dama sun mutu bayan wani ramin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ya rufta a garin Mayo Kam da ke ƙaramar hukumar Bali ta Jihar Taraba
  • Ana zargin mutane kusan 20 sun makale a ƙarƙashin ramin, yayin da ake ci gaba da aikin ceto
  • Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin jimami, yayin da aka ce mafi yawan waɗanda abin ya shafa ’yan asalin ƙauyen ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jalingo, Taraba — Mutane da dama sun mutu bayan wani ramin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba ya rufta a garin Mayo Kam da ke ƙaramar hukumar Bali ta Jihar Taraba ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru da rana yayin da masu haƙar ma’adinan ke aiki a wurin, inda mutane da dama suka makale a ƙarƙashin ƙasa.

Kara karanta wannan

An samu matsala: Mutane fiye da 30 sun mutu a ofishin hukumar NSCDC ta Najeriya

Jihar Taraba.
Taswirar jihar Taraba da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewar jaridar Punch, ana zargin mutane kusan 20 sun makale a ƙarƙashin ramin hakar ma'adanan.

Ana zargin mutane 5 sun mutu

Da yake magana da The Cable ranar Juma’a, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Taraba, Victor Mshelizah, ya ce kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane biyar yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

“Lamarin fa ya faru ne a wurin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a garin Mayo Kam da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bali.
“Ya zuwa yanzu, mutane biyar ne kawai aka tabbatar da mutuwarsu. Amma muna ƙoƙarin gano ko akwai wasu mutane da suka makale, domin mu ceto su a ramin."
“Mun riga mun tura jami’anmu wurin, kuma tun jiya muke nan muna kokarin lalubo sauran mutanen da ke ciki," in ji Mshelizah.

Al’umma ta shiga jimami

Lamarin ya jefa al’ummar garin cikin jimami, domin an ce mafi yawan waɗanda abin ya shafa ’yan asalin ƙauyen ne.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai kazamin harin da ya jawo asarar rayuka da kona gidaje

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da aka gano gawarwakin mutane 37 da ake zargi da haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a ƙauyukan M.I. Wushishi da Lukoto na Jihar Neja.

Rahotanni sun nuna cewa matasan sun mutu ne a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC).

Ramin hakar ma'adanai.
Wani bangare da ramin da mutane ke hakar ma'adanai ba nisa ka'ida ba a Filato Hoto: Simon John
Source: Getty Images

A cikin wata sanarwa da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Aniviye, ya fitar ranar Alhamis, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a yayin samamen da aka gudanar a ranakun 15 da 16 ga Satumba.

Ana cikin wannan jimamin ne kuma aka samu labarin ruftawar ramin hakar ma'adanai a jihar Taraba, wanda har yanzu ba a gama ceto mutanen da suka makale ba.

Abin da ya kashe matasa a ofishin NSCDC

Kun ji cewa sababbin bayanai sun fito kan yadda wadanda ake zargi da hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba suka rasa rayukansu a ofishin NSCDC a jihar Neja.

Wani wanda ya tsira da rayuwarsa ya yi zargin cewa waɗanda suka mutu sun shaƙe sun rasa numfashinsu bayan an cunkushe su a wani ɗaki da ba shi da isasshiyar iska.

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike, yayin da aka dakatar da Kwamandan NSCDC na Jihar Neja

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262