EFCC Ta Yi Tayin Lada ga Masu Kwarmato game da Dukiyoyin Najeriya da aka Wawure
- Hukumar EFCC ta ce za ta bai wa masu tsegunta mata bayanan kadarorin da aka wawashe wani lada mai tsoka da za a dauko daga dukiyar
- EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ya ce za a bayar da ladan tsakanin kashi 2.5 zuwa 5 cikin 100 na dukiyar da aka kwato
- Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce wasu masu ba da bayanai na iya zama hamshakan attajirai idan bayanansu suka taimaka aka kwato kadarori
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta yi tayin bai wa masu fallasa bayanai lada da ya kai kashi biyar cikin 100 na dukiyar da aka kwato.
Za su samu wannan kaso ne idan bayanan da suka bayar suka taimaka wajen gano tare da kwato kuɗaɗe ko kadarorin da ake zargin ‘yan Najeriya sun boye a ƙasashen waje.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya yi wannan bayani ne yayin da yake gabatar da lacca a taron ƙasa da ƙasa karo na 43 kan Laifukan Tattalin Arziƙi da aka gudanar a Cambridge, ƙasar Birtaniya.
EFCC za ta bada ladan kawo bayanai
A ruwayar jaridar The Cable, kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba,26 ga watan Agusta, 2027.
Olukoyede ya buƙaci mutanen da ke da sahihan bayanai kan inda ake zargin an kai ko ɓoye kadarorin Najeriya da aka samu ta hanyar cin hanci da rashawa, su tuntubi hukumar.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ina maraba da ku baki ɗaya zuwa duniyar masu fallasa bayanai. Idan wani daga cikinku ya san inda aka sace ko aka kai kadarorin Najeriya a ko’ina cikin duniya, muna da abin ƙarfafa gwiwa gare ku; tsakanin kashi 2.5 zuwa kashi 5, za a ba ku bayan an kwato kadarorin."

Kara karanta wannan
Gwamna ya dauki zafi da yan bindiga suka kai mummunan hari masallaci ana cikin Sallah
Dalilin EFCC na shirin bada ladan kwarmato
Olukoyede ya ce an samar da tsarin ne domin ƙarfafa mutane su fito su bai wa hukumar bayanan da za su taimaka wajen gano kadarorin da aka sace.
Ya ƙara da cewa ladan na iya sauya rayuwar masu ba da sahihan bayanai, har su zama hamshakan attajirai, gwargwadon darajar kadarorin da aka kwato sakamakon bayanansu.
A kalamansa:
“Idan kuka bayar da wani bayani a nan, wasu daga cikinku za su iya barin wannan wurin, su zama masu miliyoyin kuɗi a rayuwarsu."
Shugaban EFCC ya ce manufar tsarin ita ce ƙarfafa damar hukumar wajen samun sahihan bayanan sirri da za su taimaka wajen gano kadarorin da aka fitar da su daga Najeriya ta haramtattun hanyoyi.
EFCC: Dalibar BUK ta shiga matsala
A wani labarin, kun ji cewa Dalibar jami’ar Bayero, Kano, Maryam Isah Shehu, ta gurfana gaban kotun tarayya da ke Abuja kan zargin wallafa wani sako a kafar sada zumunta da ake cewa ya bata sunan EFCC.
An gurfanar da Maryam Isah Shehu ne kan wani sakon Instagram da hukumar EFCC ta ce ya kunshi zargin cewa jami’anta sun lakada wa Ahmed Uthman duka bisa umarnin wani daraktan shiyya.
Kotun ta dage sauraron bukatar belin dalibar zuwa 31 ga Agusta, bayan lauyanta ya ce ta shafe kusan kwanaki 30 a tsare kuma tana da jarabawa da ya kamata ta rubuta a lokacin,
Asali: Legit.ng

