Ana Tsoron ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Wasu ‘Yan NYSC 15 a Hanyar zuwa Abuja
- ‘Yan bindiga sun tare motar Peace Mass Transit a hanyar Ofu/Itobe-Onicha-Igo inda suka sace ‘yan NYSC
- Jami’in dan sanda ya tabbatar da cewa maharan yi wa direban motar rauni kafin su yi awon gaba da matasan
- Miyagun ‘yan bindigan sun bar wasu fasinjojin motar amma suka tafi da masu yi wa kasa hidima a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kogi - Mutane 15 masu yi wa kasa hidima ake rade-radin ‘yan bindiga sun dauke su a yankin Ofu/Itobe–Onicha-Igo a jihar Kogi.
Wannan mummunan labari da ya jawo fargaba a zukatan matasa da sauran jama’a ya faru ne a karamar hukumar Ofu da ke Kogi.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun sace masu NYSC
‘Danuwan wani daga cikin wadanda abin da ya faru da shi a hanya, ya tabbatar da haka da ya zanta da jaridar FIJ a tsakiyar makon nan.
A cewarsa, an dauke ‘yan bautar kasa ne lokacin da suke tafiya daga sansanin NYSC da ke Kolokuma/Opokuma zuwa birnin Abuja.
Matasan suna cikin ‘yan sahun Batch ‘B’ Stream II na wannan shekara ta 2026 da yanzu suka gama samun horo a sansanin hukumar NYSC.
Masu NYSC suna dawo wa daga Bayelsa
Matafiyan suna kan hanya a cikin manyan motoci biyu lokacin da aka kawo masu hari.
Wanda aka yi magana da shi ya bayyana cewa ‘danuwansa mai suna Ayodele David yana cikin matasan da ‘yan bindiga suka dauke.
Wata doguwar motar tafiya da kuma wata mai lambar 564 wannan tsautsayi ya auka masu.
Adeji Joshua wanda ‘dan sanda ne, ya tuntubi iyalin masu bautar kasar, sun shaida masa abin da ya faru ne a yankin Ofu/Itobe–Onicha-Igo.
Majiya ta ce ba a san su wane ne ‘yan bindigan da suka dauke mutanen ba, amma an ji suna magana da Hausa, Turanci da Fulfilde.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun shiga fadar Sarki, sun kashe shi bayan korafi kan ta'adinsu a Niger
Direban motar yana kwance a asibiti
Daga bayanan da aka samu daga direban motar wanda ya samu rauni sosai, matasa 15 aka sace duk da cewa su 16 aka dauko a tasha.
Premium Times ta ce bidiyon da aka samu bayan an yi ta’adin ya nuna ‘yan bindigan suna ta harbin motoci kafin su dauke mutane.
Shi dai direban motar yanzu yana asibiti domin likitoci su duba raunin da ya samu.
Da aka yi yunkurin jin ta babakin ‘yan sandan jihar Kogi ba a dace ba. A lokacin, kakakinsu, Saliu Afusat ba ta dauki wayarta ba.
Tun bayan faruwar abin, rahoton ya ce su ma kamfanin motocin Peace Mass Transit ba a same su ta lambar da ke jin motarsu ba.

Source: Getty Images
Yadda 'yan ta'adda suke samun kudi
Rahoto ya fallasa dabarun ‘yan ta’adda wajen gujewa BVN da matakan tsaro suna barna da sunan mata idan sun tashi bude akawun.
Hukumar NFIU ta tono asirin yadda 'yan ta'adda ke samun kudi intanet su yi ayyukansu a Najeriya a boye ba tare da an iya ganewa ba.
Wani lokaci miyagun sukan rika neman taimako daga kasashen waje a dandalin sada zumunta, suna karyar za a taimaka wa marasa karfi.
Asali: Legit.ng
