'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Kano, an Yi Awon Gaba da Basarake

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Kano, an Yi Awon Gaba da Basarake

  • ’Yan bindiga sun sace dagacin ƙauyen Aujarawar Alkali, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, wanda aka fi sani da Ruwata, a Gezawa
  • An sace dagacin ƙauyen ne a wani hari da ’yan bindigar suka kai yankin da daddare ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026
  • Shugaban gundumar Jogana ya buƙaci jami’an tsaro su ƙara ƙoƙari wajen ceto dagacin ƙauyen tare da tabbatar da tsaron jama’a da dukiyoyinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin ƙauyen Aujarawar Alkali da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Jihar Kano, Alhaji Ahmad Yakubu Ahmad, wanda aka fi sani da Ruwata.

An ce ’yan bindigar sun kai harin ne da daddare ranar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026, inda suka yi awon gaba da dagacin ƙauyen zuwa wani wurin da ba a san inda yake ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: An kai korafin dan majalisa gaban NDLEA kan zargin shan hodar iblis

'Yan bindiga sun sace dagaci a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An tabbatar da sace dagacin

Jaridar Leadership ta ce Mahi Isma’il, mai magana da yawun Zannan Kano kuma Hakimin Jogana, ya tabbatar da faruwar lamarin ranar Juma’a, 18 ga watan Satumban 2026.

Mahi Ismail ya bayyana sace dagacin a matsayin koma-baya ga zaman lafiya da ake samu a yankin.

A cewarsa, lamarin ya haifar da damuwa tsakanin mazauna yankin, musamman ganin yadda ’yan bindigar suka samu damar shiga garin da daddare tare da yin awon gaba da dagacin.

An nemi jami’an tsaro su ceto shi

Hakimin Jogana, Alhaji Abdulkadir Ma’aji, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara kaimi wajen ganin an ceto dagacin ƙauyen cikin ƙoshin lafiya.

“Muna roƙon jami’an tsaro su ƙarfafa tsaron rayuka da dukiyoyi, tare da yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da dawowar shugaban ƙauyenmu lafiya,” in ji Ma’aji.

An bukaci jama'a su kwantar da hankali Ma’aji ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su kasance cikin kwanciyar hankali tare da bin doka da oda yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin gano inda aka tafi da dagacin.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi maganar sayen hannun jari a matatar Dangote, ya ba 'yan Najeriya shawara

Ya buƙaci jama’a su ba jami’an tsaro duk wani bayani mai amfani da zai taimaka wajen gano ’yan bindigar da kuma ceto dagacin ƙauyen.

Haka kuma, ya ƙarfafa mazauna yankin da su ƙara taka-tsantsan tare da kasancewa cikin faɗakarwa domin kare kansu da kuma taimakawa wajen hana sake faruwar irin wannan hari.

Ko a kwanakin baya ma wasu 'yan bindiga sun hallaka wani shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano.

'Yan bindiga sun kai hari a Kano
Kwamishinan 'yan sandan Kano zaune a ofis Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kai hari gidan kwamishina

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindiga sun mamaye gidan wani kwamishina a Jihar Imo, kudu maso gabashin Najeriya, inda suka kashe wani sufeto na ’yan sanda da ke aikin gadi.

Sufeton yan sandan, Henry Effiong, yana gadin gidan Kwamishinan Kasuwanci da Zuba Jari, Rex Anunobi, lokacin da maharan suka kai masa hari tare da kashe shi.

Majiyoyi sun ce ’yan bindigar sun fara kwace makaminsa, suka karɓi bindigar da yake ɗauke da ita da kuma wayoyinsa kafin su kashe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng