Tinubu Ya Kama Sunan Buhari da Obasanjo bayan Najeriya Ta Samu Nasara a Shari'ar Mambilla

Tinubu Ya Kama Sunan Buhari da Obasanjo bayan Najeriya Ta Samu Nasara a Shari'ar Mambilla

  • Bola Tinubu ya ce nasarar Najeriya kan Sunrise Power a ICC ta nuna cewa ƙasar ba za ta amince da ikirarin cin moriyarta ba bisa hakki ba
  • Kotun ICC ta yi watsi da buƙatar Sunrise Power ta biya kamfanin dala biliyan $2.35 kan aikin samar da wutar lantarki na Mambilla
  • Kotun ta kuma umarci Sunrise Power da mai tallafa mata su mayar wa Najeriya kuɗin shari’a da suka kai $11.8m

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kam nasarar da Najeriya ta samu kan kamfanin Sunrise Power dangane da shari'ar Mambilla.

Tinubu ya ce nasarar ta nuna cewa Najeriya ba za ta mika wuya ga abin da ya kira ikirarin cin moriya da zalunci daga hukumomi da kamfanoni na cikin gida da ƙasashen waje ba.

Kara karanta wannan

Dickson: Jagoran NDC na kasa ya fadi dalilin kin shiga APC, ya aika sako ga Kwankwaso da Obi

Tinubu ya yi magana kan shari'ar Mambilla
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da aka sanya a shafin X, inda ya ce Najeriya za ta ci gaba da kare dukiyar al’ummar ƙasa daga duk wani nau’in ikirarin da bai dace ba.

ICC ta yi watsi da buƙatar Sunrise Power

A ranar Alhamis ne kotun ICC da ke Paris ta yanke hukunci a madadin Najeriya kan buƙatar Sunrise Power ta neman diyya ta dala biliyan $2.35 dangane da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla.

Kotun ta yi watsi da ikirarin Sunrise Power cewa Najeriya ta karya yarjejeniyar da ta kulla da kamfanin, ciki har da wata yarjejeniyar sulhu da ƙarin yarjejeniya da aka yi mata.

Haka kuma, kotun ta umarci Sunrise Power da mai tallafa mata su mayar wa Najeriya kuɗin da ta kashe wajen shari’ar, wanda ya kai dala miliyan $11.8.

Tinubu ya yaba wa Obasanjo da Buhari

Kara karanta wannan

Ba haka aka so ba: Saudiyya ta ki amincewa da bukatar Najeriya kan aikin hajjin 2027

Da yake mayar da martani kan hukuncin, Tinubu ya yaba wa tsofaffin shugabannin Najeriya biyu, Olusegun Obasanjo da marigayi Muhammadu Buhari, saboda bayar da shaida a lokacin shari’ar.

Ya kuma yaba wa Lateef Fagbemi, Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, da ma’aikatar shari’a ta tarayya bisa abin da ya bayyana a matsayin gagarumar gudunmawar da suka bayar wajen kare muradun Najeriya.

“Wannan sabon hukunci ya tabbatar da ƙudurin gwamnatin Najeriya na kada ta amince da ikirarin cin moriya da zalunci daga gurbatattun hukumomi ko kamfanoni na cikin gida da na ƙasashen waje, da masu taimaka musu da masu ɗaukar nauyinsu,” in ji sanarwar.

Tinubu ya yaba wa lauyoyi

Tinubu ya ce a madadin gwamnatin tarayya da al’ummar Najeriya, yana yaba wa Fagbemi da tawagar ma’aikatar shari’a bisa irin ƙoƙarin da suka yi wajen kare ƙasar.

Ya kuma yaba wa tawagar lauyoyin da suka kare Najeriya a shari’ar, ƙarƙashin jagorancin Elizabeth Oger-Gross da Tolu Obamuroh na kamfanin Paul Hastings LLP, saboda abin da ya bayyana a matsayin ƙwarewa wajen kare ƙasar.

Shugaban ya kuma yaba wa Obasanjo da Buhari saboda kishin ƙasa da goyon bayan da suka nuna, musamman kasancewarsu shaidu a shari’ar.

Kara karanta wannan

Kurunkus: Dangote ya fadi dalilin da ya sa ake sayan fetur da tsada a Najeriya

Rikicin ya shafi yarjejeniyar Mambilla ta 2003

Shari’ar ta samo asali ne daga wata yarjejeniya ta shekarar 2003 da ta shafi gina tashar samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 3,050 a jihar Taraba.

An tsara aikin ne bisa tsarin (BOT), wato gina tashar, gudanar da ita na wani lokaci sannan a miƙa ta ga gwamnati.

Tinubu ya yi magana kan shari'ar Mambilla
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Gwamnatin Tinubu za ta janye tallafin lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta sanar da shirin kawo ƙarshen biyan tallafin wutar lantarki a Najeriya daga 2027.

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta janye tallafin ne domin samar da tsarin da zai dawwama a ɓangaren wutar lantarki. Read more

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng