Yan Bindiga Sun Far wa Mutanen Garuruwa 3 da Harbi, Sun Kashe Mutane da Dama

Yan Bindiga Sun Far wa Mutanen Garuruwa 3 da Harbi, Sun Kashe Mutane da Dama

  • Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 13 a kauyuka uku da ke Masarautar Dansadau a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara
  • An kai hare-haren ramuwar gayya ne bayan ’yan sa-kai sun kashe wani jagoran ’yan bindiga da wasu yaransa
  • Mazauna yankin sun ce kusan kashi 80 zuwa 90 cikin 100 na mutanen kauyukan da abin ya shafa sun gudu zuwa garin Dansadau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - ’Yan bindiga sun kashe aƙalla mutane 13 a kauyuka uku da ke Masarautar Dansadau a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

An zargin cewa wannan harin na ramuwar gayya ne bayan ’yan sa-kai sun kashe wani jagoran ’yan bindiga da wasu daga cikin mutanensa.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani mazaunin yankin da ya yi magana da Daily Trust ba tare da bayyana sunansa ba saboda dalilan tsaro, ya yi kira da a ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An bayanan sirri kan wuraren da yan bindiga ke shirin kai hare hare a Najeriya

Yan bindiga sun kia harin ramuwa

Ya ce ’yan bindigan na zargin kauyukan uku da haɗa baki da ’yan sa-kai wajen kashe jagoran dabar su da wasu daga cikin mutanensa.

“Abin da ya faru shi ne, ’yan bindigan sun zargi kauyukan uku da haɗa baki da ’yan sa-kai, waɗanda suka kashe jagoran ’yan bindigar da yaransa,” in ji shi.

“Akwai tsananin gaba tsakanin ’yan sa-kai da ’yan bindiga, inda kowanne ɓangare ke ƙoƙarin kashe ɗayan. ’Yan bindigan sun hana mutane yin noma kwata-kwata tsawon shekaru biyu da suka gabata.”

Rahotanni sun nuna cewa ƙauyukan uku da lamarin ya shafa su ne Dandallah, Tudu Gabas da Unguwar Majidadi.

’Yan sa-kai sun kashe jagora

Mazaunin ya ce ’yan sa-kai sun yi nasarar kashe wani sanannen jagoran ’yan bindiga da wasu daga cikin mataimakansa, tare da kwashe bindigoginsu.

Ya ƙara da cewa daga bisani ’yan bindigan sun zargi kauyukan uku da tallafawa tare da ƙarfafa ’yan sa-kai wajen gudanar da samamen.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai kazamin harin da ya jawo asarar rayuka da kona gidaje

“’Yan bindigan sun ce ba zai yiwu yaran su kashe abokan aikinsu ba tare da goyon bayan dattawan kauyukan ba.
“Sun kashe mutane tara a ƙauyen Dandallah tare da jikkata wasu. An kashe mutane biyu a ƙauyen Unguwar Sarkin, sannan an kashe mutum ɗaya ko biyu a Tudun Gabas,” in ji shi.
Dauda Lawal.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal a gidan gwamnatinss da ke Gusau Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Mazauna sun tsere zuwa Dansadau

Wani mazaunin yankin da shi ma ya nemi a sakaya sunansa ya ce kusan kashi 80 zuwa 90 cikin 100 na mutanen kauyukan uku da abin ya shafa sun tsere zuwa garin Dansadau.

Ya ce ’yan bindigan sun kuma kai hari ƙauyen Dangurgu, lamarin da ya tilasta wa mazauna ƙauyen barin gidajensu.

Da aka tambaye shi game da kasancewar jami’an tsaro a yankin, mazaunin ya ce kauyukan na cikin wuraren da jami’an tsaro ba sa iya zuwa.

Sojoji sun yi luguden wuta a Zamfara

Kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta kai farmakin sama kan wata maboyar ‘yan ta’adda a Yankuzo da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Daga cikin waɗanda aka ce an kashe akwai wani ɗan ta’adda mai suna Isiya Gurgu, wanda ake zargin yana kashe kashe a yankin

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262