Allah Mai Iko: An Gano Babban Bala'in da Matukin Jirgin Sojoji Ya Kauce Wa kafin Ya Yi Hatsari
- Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce matukin jirgin sojoji da ya yi hatsari a Igbokoda ya yi matukar kokarin wajen kaucewa fadawa cikin jama'a
- Ya ce matukin jirgin ya yi kokarin kauce wa wani bala’i mafi girma ta hanyar karkatar da jirgin daga kan al’ummar garun Igbokoda
- Jirgin ATR-42 mai lambar rajista NAF 931 ya yi hatsari ranar Litinin, inda mutane 25 da ke cikinsa suka rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ondo, Nigeria - Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya ce matukin jirgin Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) da ya yi hatsari a Igbokoda ya yi kokarin matuka kafin ya mutu.
Gwamnan ya ce labarin da ya samu ya anjna matukin jirgin ya kauce wa wani bala’i mafi girma ta hanyar karkatar da jirgin daga kan al’umma kafin ya fado cikin fadama.

Kara karanta wannan
Amurka da Saudiyya sun turo muhimmin saƙo zuwa Najeriya kan hatsarin jirgin sojojin sama

Source: Facebook
Gwamnan Ondo ya kai ziyara wurin
Lucky Aiyedatiwa ya bayyana haka ne yayin da yake magana ga manema labarai da ya ziyarci wurin da jirgin ya yi hatsari ranar Laraba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Gwamna Aiyedatiwa ya ce shaidu sun shaida masa cewa jirgin ya bayyana kamar yana dosar al’ummar garin kai tsaye kafin matukin ya sauya alkiblarsa.
“Daga abin da mutanen suka gaya mana, jirgin ya kusa fadowa cikin jama'a amma matukin ya yi nasarar karkatar da shi daga nan kafin ya yi hatsari kimanin mita 200 nesa da garin, sannan ya fada kai tsaye cikin yankin fadamar,” in ji Aiyedatiwa.
Matukin ya kauce wa al’umma
Gwamnan ya ce mazauna yankin sun kuma bayar da rahoton jin wani sauti da ke nuna cewa jirgin na fuskantar matsalar inji kafin hatsarin.
“Matukin ne kaɗai zai iya bayyana ƙoƙarin da ya yi wajen karkatar da jirgin. Domin mutanen yankin sun ga jirgin ya yi kandu, tare da wani sauti kamar na injin da ya lalace,,” in ji shi.
Ayyukan lalubongawawwaki da sauran abubuwa sun shiga rana ta biyu, yayin da yanayin ƙasa mai wahala a kewayen wurin hatsarin ke ci gaba da kawo cikas wajen gano babban tarkacen jirgin, in ji rahoton Vanguard.
An gano kayayyaki da tarkacen jirgi
Aiyedatiwa ya bayyana wurin da hatsarin ya faru a matsayin “abin ban tsoro sosai”, yana mai cewa an gano kayayyakin jami’an sojoji da tarkacen jirgin, kuma an adana su domin gudanar da bincike.
“Ba a ga babban jikin jirgin ba. Ana kyautata zaton yana ƙarƙashin fadamar,” in ji shi.

Source: Facebook
Aiyedatiwa ya ce ya umarci ma’aikatar ayyuka ta jihar da ta tura manyan injina guda biyu, waɗanda aka fi sani da swamp buggies, domin sauƙaƙa isa wurin ta ruwa da kuma bai wa manyan kwale-kwale damar matsowa kusa da wurin hatsarin.
Gwamnan Ondo ya gano abubuwa 3
Kun ji cewa gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya fara hasashen matsalolin da ka iya zama sanadin faduwar jirgin rundunar sojojin Najeriya, wanda ya yi hadari a yankin kauyen Igbokoda
Gwamna Aiyedatiwa ya bayyana cewa matsalar fasaha ko ta na’ura da kuma yankewar sadarwa da hasumiyar kula da jiragen sama na iya zama sanadin hatsarin jirgin sojin saman Najeriya.
Asali: Legit.ng
