Wata Sabuwa: An Fara Batun Kauracewa Zaben 2027 kan Albashin Jami'an INEC
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na AAC, Omoyele Sowore, ya goyi bayan ƙarin albashin ma’aikatan hukumar zaɓe ta INEC, inda ya ce ya kamata su riƙa karɓar aƙalla N500,000
- Sowore ya yi gargaɗin cewa ma’aikatan ba za su iya tabbatar da sahihancin zaɓe ba idan ana biyan su albashi marar gamsarwa, yana mai cewa dole ne a inganta walwalarsu
- Wannan martani nasa ya biyo bayan furucin Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, cewa ma’aikatan hukumar na cikin waɗanda ake biyan albashi kadan a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya goyi bayan ƙarin albashin ma’aikatan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), yana mai buƙatar a riƙa biyan su aƙalla N500,000.
Sowore ya bayyana hakan ne bayan shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce ma’aikatan hukumar na cikin waɗanda ake biya kudi kadan.

Source: Getty Images
Korafin Sowore kan INEC
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore ya ce ya kamata a riƙa biyan ma’aikatan hukumar zaɓen albashi mai gamsarwa domin su iya gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ya ce:
“Dole ne a riƙa biyan ma’aikatan zaɓe albashi mai kyau. Ba za a yi tsammanin ma’aikatan INEC za su kare sahihancin zaɓe ba alhali ana biyan su albashi marar gamsarwa.”
Sowore ya ƙara da cewa ma’aikatan sun cancanci mafi ƙarancin albashin N500,000, yana mai cewa ingancin zaɓe yana farawa ne daga kyakkyawan yanayin aiki da albashin da zai iya biyan bukatun rayuwa.
Ya kuma yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da wulaƙanta ma’aikatan, zai haɗa kai da su wajen kaurace wa zaɓen 2027.
Ya ce ma’aikatan suna da ’yancin haɗa kai domin neman ingantattun sharuɗan aiki, ciki har da ɗaukar matakan ƙwadago da doka ta amince da su.
Korafin da INEC ta yi
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana matsalar albashin ma’aikatan ne a ranar Talata a Abuja, yayin wani taron manema labarai da ya yi domin bayani kan shirye-shiryen hukumar na zaɓen 2027.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Amupitan ya ce hukumar ta fara ɗaukar matakai domin inganta walwalar ma’aikatanta, yana mai cewa dole ne a samar musu da albashin da zai biya bukatun rayuwarsu.

Source: Twitter
Shirye-shiryen zaben 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa Legas ce ke da mafi yawan masu rajistar zaɓe a jihohin Najeriya.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja, inda ya ce hukumar ta kammala matakai tara daga cikin muhimman matakai 14 da aka tsara domin shirya zaɓen.
Ya kuma ce hukumar ta samar da tsarin gudanar da shirye-shiryen zaɓen a hedikwatarta, ofisoshinta na jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, tare da ofisoshi a ƙananan hukumomi 774 na ƙasar.
Asali: Legit.ng

