Kwana Ya Kare: Wani Babban Jami'i a Gwamnatin Jihar Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Wani Babban Jami'i a Gwamnatin Jihar Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ya rasa mai magana da yawunta, Saminu Yusuf Abdullahi, wanda ya rasu a safiyar Laraba bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da sallar jana’izarsa da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar yau Laraba, 7 ga watan Oktoba, 2026
  • Marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen sanar da jama’a ayyukan hukumar da kuma karbar bayanan gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya riga mu gidan gaskiya da sanyin safiyar Laraba, 7 ga watan Oktobaz 2026.

Bayanai da muka samu sun nuna cewa Saminu Yusuf ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Kano.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Tribune Nigeria ta ruwaito cewa n tabbatar da rasuwar Saminu ne a cikin wata sanarwa da Shugaban ofishin hukumar Kashe Gobara na ƙaramar hukumar Dambatta, PFS2 Muhammad Ibrahim-Nasiru, ya fitar ga manema labarai a Kano.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi alhini da Allah ya yi wa sakataren Majalisar shari'ar Musulunci rasuwa

Kakakin hukumar kashe gobara ya rasu

A cewar sanarwar, an gudanar da sallar jana’izar Saminu Yusuf Abdullahi da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar yau Laraba kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Marigayin ya kasance kakakin Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen isar da bayanan ayyuka da ayyukan ceto na gaggawa na hukumar ga jama’a a tsawon lokacin da ya yi yana bakin aiki.

Sanarwar ta ce Saminu ya yi fice musamman wajen samar da bayanai cikin lokaci kan gobara, matakan kariya, ayyukan ba da agajin gaggawa da sauran ayyukan da suka shafi kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

“Mun ɗauki rasuwarsa a matsayin babban rashi ga Jami’an Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano da ma al’umma baki ɗaya, musamman duba da rawar da ya taka wajen sanar da jama’a a lokacin da ake fuskantar yanayin gaggawa,” in ji sanarwar.

Abokan aikinsa sun yi jimami

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027 da magana: Goodluck Jonathan ya fara yi wa APC 'aiki'

Sanarwar ta ƙara da cewa abokan aikinsa da sauran masu ruwa da tsaki sun fara jimamin rasuwarsa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Jami'an hukumar kashe hobara da suka yi aiki tare da sun fara bayyana alherin marigayin tare da amincewa da gudunmawar da ya bayar wajen kare lafiyar jama’a da sadar da bayanan gaggawa.

Saminu.
Mai magana da yawun hukumr kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi Hoto: Auwal Ibrahim
Source: Facebook

Ana ganin rasuwar Saminu Yusuf Abdullahi ta zama babban gibi ga harkokin sadarwar jama’a na hukumar kashe gobara, inda ya kasance wata muhimmiyar hanyar haɗa hukumar agajin gaggawa da jama’a a lokacin gobara da sauran yanayin gaggawa.

Gwamnan Kano ya mika sakon ta'aziyya

Kun ji cewa gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar, Alhaji Sani Lawan Kofar Mata.

Gwamna Abba ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai, ‘yan uwa, abokan hulɗa da al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar Alhaji Sani Lawan Kofar Mata, yana mai cewa rasuwarsa babban rashi ne.

Ya yaba da irin hidima da dumbin gudummuwa da marigayin ya bayar tare da kula da jin daɗin al’umma, musamman a fannin harkokin alhazai na jihar Kano lokacin da yake aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262