Zamfara: Ƴan Majalisar da Suka Bar APC Suna Tattaunawa da Jam'iyyun Adawa 3
- ’Yan majalisar Zamfara bakwai da suka fice daga jam'iyyar APC sun ce suna tattaunawa da wasu jam'iyyun adawa domin sanin makomar siyasarsu
- Ibrahim Tukur Bakura ya ce PDP ma ta tuntube su, amma ba su gudanar da ganawa ta hukuma ba, yayin da suke neman shawarar al’ummar Zamfara
- ’Yan majalisar sun ce za su sanar da jam’iyyar da za su koma nan da mako mai zuwa, bayan kammala nazari da tuntubar jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara- ’Yan majalisar dokokin Zamfara bakwai da suka yi murabus daga APC sun bayyana cewa suna tattaunawa da jam’iyyun adawa.
Majiyoyi sun tabbatar da daga cikin jam'iyyun da suke tattaunawa akwai ADC, NDC da PRP kan makomarsu ta siyasa kafin zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara.

Kara karanta wannan
Siyasar Arewa: An fara tono laifin 'yan Majalisar dokoki 8 da suka fice daga jam'iyyar APC

Source: Facebook
Jam'iyyun da yan majalisar ke tattaunawa da su
Daya daga cikin ’yan majalisar, Ibrahim Tukur Bakura, ya ce sun tattauna da jam’iyyun uku, yayin da PDP ma ta tuntube su amma ba a yi ganawar hukuma ba, cewar Daily Trust.
Bakura ya ce za su yi taka-tsantsan wajen zabar jam’iyyar da za su koma, domin yin la’akari da ra’ayin al’ummar jihar Zamfara da bukatun mazabunsu kafin yanke hukunci.
Ya ce ba za su yi gaggawar yanke shawara ba, inda ya tabbatar da cewa za su sanar da matsayinsu nan da mako mai zuwa abin da suke ganin ya fi dacewa da su a siyasa.
Bakura ya kara da cewa kofarsu a bude take domin tattaunawa da duk wata jam’iyya da ke sha’awar karbarsu, yayin da suke neman yi wa al’ummarsu hidima.
Ya ce tuni sun fice daga APC tare da fara tattaunawa da wasu jam’iyyun siyasa, kuma za su kammala zaben inda za su nufa kafin mako mai zuwa.

Source: Original
Wasu daga yan majalisar da suka bar APC
’Yan majalisar sun hada da Bashir Aliyu Gummi, Nasiru Abdullahi, Bashir Masama, Faruku Dosara, Ibrahim Tukur Bakura, Shamsudeen Hassan da Bashiru Sarkin-Zango.
A makon da ya gabata ne ’yan majalisar bakwai suka sanar da ficewarsu daga APC, ba tare da bayyana jam’iyyar da za su koma nan take ba, kamar yadda Tribune ta ce.
A baya, majalisar dokokin Zamfara ta dakatar da ’yan majalisar bisa zargin aikata rashin da’a, hada baki, barna da kuma gudanar da zaman majalisa ba bisa ka’ida ba.
Sababbin jihohi: Gwamna Dauda ya ba da shawara
A baya, mun ba ku rahoton cewa gwamnan Zamfara Dauda Lawal ya ba da shawara ga Gwamnatin Tarayya kan shirin kirkirar sababbin jihohi a Najeriya.
Lawal ya ce matsalolin kudi da jihohin Najeriya 36 ke fuskanta sun sanya bukatar karin jihohi zama abin da ya kamata a sake tunani kafin aiwatar da wannan shiri.
Gwamnan ya ce Zamfara ta samu ci gaba tun bayan kirkirarta, musamman wajen aikin yi, bunkasar birane da noma da kuma sauran ci gaba a bangarori da dama.
Asali: Legit.ng
